Jami’in cibiyar gudanar da bincike kan masu dauke da cutar kanjamau na Najeriya (NAIIS) Adebobola Bashorun ya bayyana cewa NAIIS ta kammala gudanar da bincike a jihohi 16 na kasar nan.
Bashorun ya fadi haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Ya ce gwamnati ta yardar wa wannan cibiya ta gudanar da bincike kan wadananan cututtuka tun a ranar 28 ga watan Yuni domin sanin adadin yawan mutanen dake dauke da cututtukan kanjamau, hepatitis B da C don samar musu da kulan da suke bukata a kasar.
Bashorun ya ce jihohin da suka kammala wannan bincike sun hada da Kaduna, Adamawa, Enugu, Bauchi, Gombe, Abuja, Nasarawa, Kwara, Kano, Jigawa, Legas, Ogun, Ondo, Anambra, Cross Rivers da Rivers.
Sannan suna gab da kammala aiyukkan a jihohin Taraba, Imo, Sokoto, Neja, Ekiti da Bayelsa.
Ya ce a dalilin rikicin da ake fama da su a jihohin Barno, Filato da Yobe cibiyar bata iya yin irin wadannan bincike a wadannan jihohi ba. ” Da zarar komai ya natsa zamu tafi wadannan jihohi.