Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jinjina wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles bisa kokarin da suka yi har suka zama na biyu a wasan cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala ranar Lahadi.
Shettima wanda shima ya halarci filin wasan daga Najeriya domin kallon wasan karshe tsakanin Najeriya da mai masaukin baki wato kasar Cote D’Voire ya yaba da kokarin da Eagles din suka yi.
” Yau naka ne gobe na wani, yau ina su kasar Masar, Morocco da sauran manyan kasashen da suka halarci gasar, duk an cire su amma mu mun kai har karshe, ashe hakan abin a yaba muku ne sannan kuma abin farinciki a gareku.
” Ina kira gareku da ku yi hakuri ku gode wa Allah da ya kai zuwa har matakin karshe. Abinda za mu yi shine mu kara shiri, mu duba mu kuma fara kokarin tunkarar abinda ke zuwa nan gaba.
Idan ba a manta ba Giwayen Cote D’Voire sun murkushe Shahunan Najeriya a wasan karshe na cin kofin nahiyar Afirka, AFCON.
Najeriya ce ta fara jefa kwallo a ragar Cote D’Voire, sai dai kuma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sai giwayen suka fusata suka fara bin shahunan daya bayan daya suna murkushe su.
A karshe dai an tashi wasa 2-1.
Discussion about this post