Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwa dangane da abin da ka iya samun ‘yan Najeriya mazauna Afrika ta Kudu, bayan karawar da Super Eagles za ta yi da Bafana Bafana a ranar Laraba.
Najeriya za ta kece raini a wasan kusa da na ƙarshe tsakanin ta Afrika ta Kudu.
“An ja Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Pretoria, babban birnin Afrika ta Kudu, dangane da wasu kalamai masu neman tayar da tarzoma da wasu ‘yan ƙasar ke watsawa kan ‘yan Najeriya mazauna ƙasar.”
Ta ce wannan barazana da ake wa ‘yan Najeriya ta taso ne a saboda karawar da Super Eagles za su yi da Bafana Bafana, a Gasar AFCON, a ranar Laraba, 7 ga Feburairu.
“Yawancin rubuce-rubuce da ‘yan Afrika ta Kudu ke yi kan ‘yan Najeriya mazauna ƙasar su, abin tayar da hankula ne.
“Su na cewa za su jibgi ‘yan Najeriya idan Super Eagles ta yi nasara kan Bafana Bafana.”
Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Afrika ta Kudu na jan hankalin ‘yan Najeriya mazauna Afrika ta Kudu cewa su guji furta kalaman harzuƙa abokan hamayya. Kuma su tabbatar sun kalli wasan a wurin da babu barazana ga rayukan su.
An kuma shawarce su kada su riƙa ihu da sowa da hayaniyar da ka iya harzuƙa ‘yan Afrika ta Kudu, idan har Najeriya yi nasara a kan su.
Ana jan kunnen su da cewa su kasance masu bin doka da oda, kuma su kai rahoton duk wani ko wasu da ke wa lafiya, dukiya ko rayuwar su barazana.
Discussion about this post