Kaftin mai riƙon kambu na ‘yan wasan Najeriya, Super Eagles a Gasar AFCON 2023, William Troost-Ekong, ya yaba dangane da irin goyon baya da karfafawar da suka samu daga Shugaba Bola Tinubu, wanda ya biya dukkan alawus-alawus da suke bi har Naira biliyan 12.
Baya ga biyan su alawus-alawus ɗin, Tinubu ya kira su ya ƙarfafa masu guiwa kafin fara karawar su da Angola.
Haka shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar LP, Peter Obi, dukkan su sun hallara a filin wasa na Houphouet-Boign da ke Abidjan, babban birnin Cote de Ivoire a ranar Juma’a.
An riƙa watsa bidiyon Peter Obi tsaye a tsakiyar magoya bayan Super Eagles, maimakon ya zauna wurin manyan baƙi.
Yayin da wasu ke ganin cewa irin wannan zai ɗauke hankulan ‘yan wasa daga maida hankali su buga ƙwallo, shi kuwa Troost-Ekong ya ce sun yi farin ciki sosai.
Sai dai kuma ya ce kamata ya yi a nuna masu irin wannan goyon baya da ƙarfafawar tun a farkon fara gasar.
“Shugaba Tinubu ya yi mana fatan alheri. Ina ganin hakan abu ne mai kyau sosai. Ina ma a ce mun samu irin wannan goyon bayan tun a wasannin mu na farko.”
“Ina ganin mutane da yawa za su ci gaba da zuwa. Hakan kuwa zai sa mu ma mu riƙa tutiya da tinƙaho.”
Da aka tambaye shi ko halartar da irin su Akpabio da Peter Obi suka yi a stitadiyan zai iya ɗauke masu hankali daga wasa, Troost ya ce “ko kaɗan, ai sun zo ne domin ba mu goyon baya.”
Discussion about this post