Kafɗin din Super Eagles ya bayyana cewa suna sa ran Najeriya ta yi nasara a wasan ƙarshe na cin kofin kwallon kafa na kasashen nahiyar Afrika.
Yau Lahadi ne za a buga wasan ƙarshe tsakanin Najeriya da mai masaukin baƙi, Cote D’Voire.
Ahmed Musa wanda ake sa ran a yau ne zai buga wasa na farko tunda aka fara wasan ya ce burin sa shine ya yi nasarar cin kofi a karo na biyu wa Najeriya.
” Lallai wasan zai bamu wahala, amma fa ina tabbatar muku cewa idan Allah ya bamu nasara, abu ne da zan yi alfahari da shi matuƙar gaske.
” Zai zamo na yi nasarar cin kofin sau biyu kenan, kuma nasarar zai kawo mana ci gaba masu ma’anar garke.
Musa ya bayyana haka ne da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai ranar Asabar.
Discussion about this post