Shugaban CAF Patrice Motsepe ya ayyana gasar AFCON 2023 da ke gudana a matsayin “mafi kyawun tsarin da Nahiyar Afirka ta shirya,” tare da yabawa gudunmawar da kungiyar Super Eagles na Najeriya, da mai masaukin baki, Cote d’Ivoire da dukkan sauran kungiyoyin da suka shiga gasar suka bayar.
Yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida a Abidjan a ranar Alhamis, Motsepe ya bayyana kwarin gwiwarsa kan wasan karshe da za a yi a ranar Lahadi, inda ya kara da cewa shugaban Najeriya Bola Tinubu zai kasance cikin manyan baki da za su halarci kasar ranar don kallon wasan karshe.
Motsepe ya bayyana cewa, “An gaya mani cewa shugaban Najeriya zai zo,” Ina zaune kusa da mataimakin shugaban kasa (Kashim Shettima) yayin wasan Najeriya da Afirka ta Kudu. yana iya ganin farin cikina. Kuma eh, koyaushe ina cikin farin ciki!”
Motsepe ya ci gaba da nuna jin dadinsa ga Najeriya, inda ya ce, “Idan ba ka je Legas ba, ba ka je Afirka ba, ina jinjina wa Najeriya.
Baya ga mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima da ya halarci fafatawar Najeriya da Bafana na Afirka ta Kudu, gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da takwaransa na Bayelsa Douye Diri su ma sun halarci kallon wasan.
Haka shima shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya halarta tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour 2023 Peter Obi da sauran ‘yan siyasa da dama.
Discussion about this post