Ƴan wasan Super Eagles su yi addu’o’i na musamman domin waɗanda suka rasu a lokacin da za a buga fenariti tsakanin su da Bafana Bafana a wasan kusa da na ƙarshe.
Tsohon ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Delta, Cairo Ojougboh ya rasu sakamakon bugun zuciya da ya same shi a daidai za a buga fenariti tsakanin Najeriya da Afirka Ta Kudu.
Ojougboh ya yanke jiki ya ya faɗi ya yi sallama da duniya a daidai za afara buga daga kai sai mai tsaron gida a wasan.
Kafin ya rasu Ojougboh dan jam’iyyar APC ne kuma mai yawan tofa albarkacin bakinsa kan duk abinda da za tattauna a zauren Majalisar.
Discussion about this post