Kungiyoyin bada tallafi ne ke kula da masu dauke da cutar kanjamau a Najeriya

0

Jami’in cibiyar kare jarirai kamuwa da cutar kanjamau tun daga cikin uwayen su (PMTCT) da Shirin hana yaduwar cutar kanjamau da cutar sanyi na ma’aikatar kiwon lafiya (NASCP) Ijaodola Olubenga ya bayyana cewa Najeriya na samun tallafin kashi 95 bisa 100 daga kungiyoyin bada tallafi domin kula da masu fama da cutar kanjamau.

Olugbenga ya bayyana haka ne a taron wayar da kan mutane game da kare jarirai daga kamuwa da cutar kanjamau daga cikin uwayen su da UNICEF da CRIB suka shirya a jihar Rivers.

Ya ce a lissafe gwamnatin kasar Amurka na talafa wa Najeriya da kashi 75.5 na kudaden kula da masu dauke da cutar kanjamau, asusun duniya na bada tallafin kashi 17.4, kungiyar AHF na bada kashi 1.2 sannan gwamnatin tarayya na bada kashi 5.4.

Olugbenga ya ce ci gaba da haka zai kawo matsala musamman idan wadannan kungiyoyin bada tallafin suka janye tallafin su.

Ya ce a yanzu haka bincike ya nuna cewa kashi 40 bisa 100 na mutanen dake dauke da cutar kanjamau ne ke samun magungunan cutar a Najeriya.

Ya kara da cewa hakan zai hana kasar yawan dogaro da tallafin da take samu daga kungiyoyin bada tallafi musamman idan sun janye tallafin.

A karshe Olugbenga ya kuma yi kira ga gidajen yada labarai kan yin rahotannin da zai tilasta wa gwamnati kan yin abinda ya kamata da bada bayanan aiyukkanta game da kula da masu dauke da cutar kanjamau a kasar nan.

Share.

game da Author