RIGAKAFIN SHAWARA: Za a yi wa yara miliyan 1.6 allura a jihohi uku na kasarnan

0

Gwamnatin tarayya ta hada hannu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, Gavi da ‘Vaccine Alliance domin yi wa mutane miliyan 1.6 allurar rigakafin cutar shawara a jihohi uku na kasar nan.

A takarda da WHO ta raba wa manema labarai a Abuja za a fara yi wa yara ‘yan watanni tara zuwa masu shekaru 44 rigakafin ne daga ranar 7 zuwa 16 ga watan Satumba.

Allurar rigakafin zai gudana ne a kananan hukumomi uku a jihar Ebonyi, biyu a jihar Benuwai sannan daya a Cross Rivers.

Darektan hana yaduwar cututtuka da yin allurar rigakafi na hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (NPHCDA) Joseph Oteri da jami’in WHO sun yi kira ga mutanen yankunan da za a yi wa rigakafin da su fito kwansu da kwarkwata domin ayi musu allurar.

Cutar shawara

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar cewa ctar ya bullo a jihar Ebonyi a kananan hukumomi takwas.

Ma’aikatar ta bayyana cewa daga cikin mutane 55 da aka gwada daga wadannan kananan hukumomin an samu tabbacin cewa mutane tara na dauke da cutar sannan har mutane 20 sun rasu.

Sannan kuma idan ba a manta ba tun a watan Satumba 2017 zuwa Disemba 2018 ne Najeriya ke fama da bullowar cutar a wasu kananan hukumomin jihar.

Bisa ga sakamakon binciken da hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta gudanar mutane 78 na dauke da cutar a jihohi 14 a kasar nan.

Wadannan jihohi kuwa sun hada da Kwara,Kogi,Kano,Zamfara,Nasarawa,Neja,Katsina,Edo,Ekiti,Ribas,Benuwai da babban birnin tarayya Abuja.

Share.

game da Author