A ci gaba da gwagwagwar karanta shari’a da Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ke yi, kotun ta yi watsi da ikirarin da PDP da dantakarar ta Atiku Abubakar suka shigar cewa wai sakamakon zaben da rumbun tattara zabe a Intanet ya nuna shine ya yi nasara ba Buhari ba.
Kotu ta ce babu inda aka rubuta a dokar kasa da dokar hukumar zabe cewa za a bayyana sakamakon zabe ta intanet wato tun farko a tattara shi a rumbu kafin a bayyana.
Sannan kuma har iyau dokar bata bayyana a wani sashe ko wuri ba inda na’urar tantance masu zabe ya maye gurbin rajistan zabe ba.
A dalilin haka duk wani sakamako da ba ta yadda tsarin dokar kasa ta bayyana ba ne bashi da tasiri, inganci da ma’ana a gaban wannan kotu.
” Mu a kotu iyakan mu mu fede biri daga kai har wutsiya amma bamu da ikon yin doka, wannan ba namu bane.
INEC ta karbi Naira Biliyan 1.47 domin bude rumbun ajiyar bayanai, ‘server’ – Bincike
Idan ba amanta ba a watan Juni Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana wa Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa cewa ba ta mallaki wani runbun tattara bayanan sakamakon zabe da a Turance ake kira ‘server’ ba.
Wannan bayani ya biyo bayan karar kalubalantar zaben shugaban kasa da PDP tare a dan takarar ta Atiku Abubakar suka shigar da APC, Shugaba Muhammadu Buhari da kuma INEC kan ta.
A cikin karar da Atiku ya shigar, ya yi ikirarin cewa sakamakon da INEC ta bayyana daban, wanda ke cikin rumbun tattara sakamakon zaben ta kuma, wato ‘server’ daban.
Atiku ya yi ikirarin cewa shi ne ya yi nasara a kan Buhari da ratar kuri’u masu yawa, kamar yadda ya ce ita ‘server’ din ta nuna.
Daga nan PDP da Atiku sun nemi kotu ta ba su damar duba wannan rumbun ajiyar kididdigar alkaluman zabe, wato ‘server’ da suka yi ikirarin INEC ta mallaka.
Sai dai kuma lauyan INEC a wancan lokacin mai suna Yunus Usman, ya roki kotu ta yi watsi da wannan zargi, domin har ma gara tatsuniya da shi. Ya ce INEC ba ta da wata ‘server’ da ta tattara sakamakon zabe, kamar yadda PDP da Atiku suka yi zargi.
Mun aika da sakamakon Zabe rumbun tattarawa dake Abuja ta Na’ura – Malaman Zabe
Ba za mu bada abinda bamu da shi ba
Lauyan INEC Usman ya ci gaba da cewa abin akwai daure kai, domin Atiku da PDP na son INEC ta ba su abin da ba ta da shi, kuma abin da ba ta taba yi ba, ballantana har a ce INEC ta mallake shi.
“Su fa so suke yi mu ba su abin da mu kuma ba mu da shi.” Inji Usman.
Daga nan kuma ya jawo hankalin kotu a kan hukuncin da ta yanke ranar 6 Ga Maris, inda ta bai wa PDP damar duba kayan da aka gudanar da zaben 2019, wanda babu maganar rumbun tattara sakamako, wato ‘server’ a ciki a lokacin.
Dukkan lauyoyin Shugaba Buhari, wato Wole Olanipekun da kuma na APC, wato Lateef Fagnemi sun nemi a kori rokon da PDP da Atiku suka yi.
Zargin da PDP da Atiku suka yi ya nuna a cewar su sun samu bayanan sakamakon zaben da suke ikirari ne a cikin wannan rumbun ajiya mai lamba: “INEC_PRES_RSLT_SRV2019, kuma mai adireshin Mac 94-57-A5-DC-64-B9 wanda ke da lambar Microsoft ID 00252-7000000000-AA535.” Inji su Atiku.
Discussion about this post