ZAZZABIN LASSA: EU za ta tallafa wa Najeriya da Naira miliyan 32 don korar cutar

0

Tarayyar Kasashen Turai za ta tallafa wa Najeriya da Naira miliyan 32 domin korar zazzabin lassa a kasar.

Kungiyar ta sanar da haka ne a wani takarda da PREMIUM TIMES ta gani ranar Alhamis.

Sakon dake cikin takardar sun nuna cewa za a yi amfani da wadannan kudade ne domin tallafa wa wadanda suka kamu da cutar a kasar nan.

Sannan kuma a inganta aiyukkan da kungiyar jinkai na ‘Red cross International’ da aiyukkan ma’aikatan kiwon lafiya dake gudanar da bincike domin gano wadanda ke dauke da cutar da wadanda za su iya kamuwa da cutar a dalilin zama kusa da wadanda suka kamu.

“Za a fi bada karfi ne wajen ganin an wayar da kan mutane kan hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar tare da raba magungunan kashe bera da sauran dabarun hana bera zama a cikin gidajen mutane a jihohin Ondo, Edo, Kano, Ebonyi,Taraba da Bauchi.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa an samu kari a yawan mutanen da suka kamu da cutar da yawan wadanda suka rasu tun da cutar ta bullo a watan Janairu.

Hukumar ta ce a ranar 16 ga watan Fabrairu adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya karu daga 109 zuwa 115.

Haka kuma ya sa aka samu karin yawan mutanen da suka rasu a sanadiyyar kamuwa da cutar daga 70 zuwa 103.

Hukumar ta bayyana cewa an samu wannan kari ne a dalilin rashin bada rahotannin adadin yawan mutanen da suka rasu da yawan wadanda ke fama da cutar.

Duk da haka hukumar ta ce an samu wannan kari ne daga jihohi 17 a kasar nan da suka hada da jihohin Ondo, Edo, Ebonyi, Kano, Kogi, Kaduna, Taraba, Plateau, Bauchi, Enugu, Abia, Benue, Borno, Gombe, Sokoto, Legas da jihar Katsina.

Rahotan ya kuma nuna cewa wasu ma’aikatan kiwon lafiya biyu sun rasu a sanadiyyar kamuwa da cutar a jihohin Bauchi da Katsina.

Hakan ya kawo jimlar adadin yawan ma’aikatan kiwon lafiya da suka rasu a dalilin kamuwa da cuta zuwa 20.

Hukumar ta kuma ce har yanzu jihohin Edo, Ebonyi da Ondo ne suka fi yawan masu fama da wannan cutar.

Share.

game da Author