Mahara sun sace jami’an tsaro hudu a jihar Kogi

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta sanar cewa mahara sun sace wasu jamin tsaron Sibul Difens, dake aiki a jihar ranar laraba.

Su dai wadannan jami’an tsaro suna hanyarsu ne na zuwa rubuta jarabawar karin girma a garin Makudi, jihar Benuwai.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kogi, William Aya ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun gaggauta garzayawa wannan wuri da aka arce da jami’an tsaron da wasu matafiya domin far farautan maharan.

Sai dai kash, ko da suka isa wannan wuri dake titin Alo- Offoke da garin Ayingba, sai suka iske motocin haya biyu duka babu kowa a ciki.

Daya daga cikin motar ma an harbe jikinta da harsashi da dama. Sai kuma rigar aiki na jami’an da aka waske da, da kuma kayan matafiya warwatse a kasa.

Aya ya ce rundunar ‘yan sanda a jihar zata rika yin sintiri da jiragen sama domin gano maboyan masu garkuwa dake addabar mutane musamman matafiya a jihar.

Titin Lokoja ya zama dandalin masu garkuwa da mutane a Najeriya inda a koda yaushe za kaji sanarwar an yi garkuwa da wani ko wasu.

Haka matsalar tsaro yake a wasu sassan kasar nan inda hare-hare da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare. Mutane da dama na tsoron bin manyan hanyoyin Najeriya a dalilin hare-haren masu garkuwa da mutane.

Hakan yasa duk da kurin da gwamnati ke yi cewa ta kusa gano bakin zare a harkar tabarbarewar tsaro a kasar nan, yana neman ya zama duk tatsuniya.

Share.

game da Author