Ba aikin inganta NTA talbijin kadai zan yi da bashin naira milyan 500 ba – Minista Lai

0

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa ba ga aikin inganta Gidan Talbijin na NTA kadai zai kashe kudaden bashin dala milyan yan 500 ba, idan ya karbo.

Ya ce ya na son ciwo bashin ne domin gudanar da wasu muhimman ayyuka a fannoni uku a ma’aikatar sa.

Lai ya yi wannan karin haske a ranar Laraba, a wani taron manema labarai, a Abuja.

Tun bayan bayyana sanarwar cewa Lai ya je Majalisar Dattawa domin neman su amince masa ya ciwo bashin dala milyan 500.
An ruwaito ya na cewa idan aka inganta Gidan Talbijin na NTA da kudaden bashi ko lamuni, to NTA za ta iya gogayya da irin su CNN da sauran su.

Sai dai a taron manema labarai din da ya kira a ranar Alhamis, Lai ya ce yanzu lokaci ne da labaran buyagi na soshiyal midiya ke neman danne sahihan labarai.

Shi ya sa inji shi, aka yi wa labarin lamunin da ya je nema wata kakkatacciyar fahimta.

“Ba daidai ba ne a rika yin rahoton cewa zan kashe dukkan kudaden ramce idan an karbo a wajen inganta talbijin ta kasa kadai ba.”

Ya ce a cikin kudin za a kafa cibiyar inganta karfin kafaden yada labarai na talbijin, wato ITS.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Minista Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya roki Majalisar Dattawa ta gaggauta amince masa ya ciwo bashin dala milyan 500, domin inganta tashoshin Gidan Talbijin na Najeriya (NTA), zuwa na zamani.

Da ya ke bayyana dalilan ciwo bashin ranar Talata a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai Lura da Basussuka, Lai ya ce idan aka amince ya ciwo bashin, za a karkata tashoshin NTA na fadin kasar nan daga tsohon yayi zuwa na zamani, wato daga ‘analogue zuwa digital’.

Ya ce hakan ya zama wajibi domin ITU ta bayar da wa’adin da ta ce kowace tashar talbijin ta koma nuna shirye-shiryen ta ta hanyar zamani, wato ‘digital’.

“Idan aka ramto kudin za a gyara tashoshin talbijin, a kafa Cibiyoyin Horas da Aikin Sadarwa da Al’adu a fadin kasar nan, wadanda za su rika horas da shirin talbijin da finafinai da kuma samar da kudin shiga.”

Minista Lai ya ce wannan gagarimin shiri zai kuma samar wa matasa 100,000 aikin yi a fadin kasar nan. Kuma zai sa a rika kallon NTA a manhajar zamani ta ‘digital’ a kowane kauye a kasar nan.

Lai ya na cikin ministoci hudu da jihohi uku da suka je Majalisar Dattawa a ranar Talata domin kare dalilan su na neman ciwo bashi.

Sauran jihohin sun hada da Kogi, Kaduna da kuma Katsina.

Cikin makonni biyu da suka gabata, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nuna damuwa dangane da tulin bashin da Najeriya ke ciwowa.

Ko a ranar Talata sai da Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta garzaya Majalisar Dattawa domin su amince Najeriya ta kara ciwo bashin dala biliyan 22.8.

Share.

game da Author