Gogarman dillacin kudaden harkalla, kuma dan-Sambon jigilar makudan kudade zuwa kasashen waje a zamamin gwamnatin marigayi Sani Abacha, wato Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Bagudu a yanzu dai ba shi kamuwa, saboda rigar kariyar mukamin gwamna da ya ke rataye a wuyan sa.
A yanzu daidai lokacin da Bagudu ke rike da akalar mulki, kuma ya ke da iron kai hannun sa a kan kudaden al’ummar Jihar Kebbi, Amurka da Tsibirin Jersey sun maido wa Najeriya naira bilyan 112.05, kwatankwacin dala milyan 308, wadanda Abacha ya sata, aka bai wa Atiku Bagudu a wancan lokacin ya loda, ya yi jigilar fitar da su kasar Amurka da Jersey.
Wane Ne Gwamna Bagudu?
Kafin ya zama Gwamnan Jihar Kebbi, Bagudu ya yi sharafi a zamanin mulkin Abacha, inda ya zama gazagurun dillalin da ya rika yi wa Abacha jidar makudan kudade ana kimshewa kasar waje.
Bagudu ya taka gagarimar rawa wajen lodi, jigila, jida da kuma karakainar kimshe kudade da karkatar da su a madadin Abacha, shaugaban mulkin soja wanda ya rasu cikin 1998.
An kiyasta akalla an karkatar da dala bilyan 2.2 a lokacin.
Wadannan makudan kudaden da aka maido wa Najeriya dai an tabbatar da cewa su ne mafi yawa da Tsibirin Jersey ya taba maida wa kasar da aka sato kudin a tarihi.
Haka dai aka bayyana a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Litinin tsakanin gwamnatin Najeriya, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da kuma gwamnatin Tsibirin Jersey.
Gwamna Ko Gogarma: Milyoyin Dalolin Da Bagudu Ya Taba Gudu Da Su
Wadannan makudan kudaden da za a maido wa Najeriya har naira bilyan 112, ba a fa lissafa da wasu maira bilyan 59.3 ba, wadanda Bagudu ya amince zai maido wa Najeriya tun a cikin 2003.
Atiku Bagudu ya amince zai maida kudin Najeriya cikin 2003, a bisa yarjejeniyar cewa Tsibirin Jersey ta rufa asiri a janye sammacin da kasar ta tura Amurka, inda kasar ta Jersey ta nemi Amurka ta kama mata Bagudu ta mika shi domin ya fuskanci hukuncin laifin harkalla a can kasar ta Jersey.
Wannan lamari ya faru a lokacin da Atiku ke Amurka a zaune.
Cikin watan Satumba, 2019 PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Atiku Bagudu ya shafe watanni shida a tsare a Amurka. Bayan ya amince zai maida wa Najeriya dala milyan 163, an sake shi a matsayin beli.
Sai dai kuma ya arto zuwa Najeriya, inda ba a sake bincikar sa ba. Maimakon haka, sai aka wanke shi, ya shiga takarar siyasa, har aka zabe shi ya zama sanata, daga nan kuma ya yi takarar gwamna a 2015 da 2019, kuma duk ya yi nasara.
Yadda Gwamnan Kebbi, Bagudu ya taba shafe wata shida a kurkukun Amurka
Jami’an tsaron kasar Amurka sun taba tsare Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu a kurkuku, tsawon watanni shida. An tsare shi ne saboda rawar da ya taka wajen yi wa tsohon shugaban Mulkin Soja, Janar Sani Abacha aikin fito da dillancin fitar da kudaden sata daga Najeriya zuwa kasashen waje.
An kiyasta cewa Abacha ya saci akalla dalar Amurka bilyan 2.2 daga baitilmalin Najeriya a lokacin da ya ke mulki. Ya rasu cikin 1998.
Takardun bayanan kotu da ke hannun PREMIUM TIMES sun nuna cewa Bagudu shi ne babban kartagin da ke fitar wa Abacha da kudade zuwa kasashen ketare.
Bagudu ya rika yin wannan harkalla tare da wasu ‘yan uwan sa ko iyalan sa, wasu jami’an gwamnati na lokacin Abacha da kuma dan Abacha, Mohammed.
Sun rika amfani da sunayen wasu kamfanoni na bige ko bogi, suna karkatar milyoyin daloli zuwa kasashen ketare.
Shi ko Abacha ne da kan sa suka mallaki wasu asusun ajiyar da aka rika kimshe kudaden a waje.
Irin rawar da Bagudu ya taka wajen yi wa Abacha dillancin fitar da kudade daga Najeriya zuwa kasashen ketare, na nan a rubuce a cikin wata kara da aka shigar a Amurka da kuma Tsibirin Bailiwick da ke Jersey. Wannan wuri kebantacce ne da ke karkashen Channels Island wanda ke karkashin mulkin mallakar Birtaniya.
Abin da yawancin ‘yan Najeriya ba su sani ba shi ne, Bagudu wanda a yanzu ya na da rikar sulken kariyar hukunci a matsayin sa na gwamna, ya taba shafe watanni shida a tsare a kurkukun Amurka.
An tsare shi ne saboda rawar da ya taka wajen satar kudaden Najeriya ya na karkatarwa ketare a madadin Abacha.
Masu bincike a Birtaniya da Amurka sun hakkake cewa Bagudu sai da ya rika amfani da matar sa da kuma wani dan uwan sa mai suna Ibrahim, wajen taimaka masa yin wannan harkalla.
Cikin 2003, wato shakeka biyar bayan mutuwar Abacha, an gano wasu dimbin kudaden da Abacha ya sata su na kimshe ne a Jersey, inda Bagudu ya maida tamkar garin su.
Nan da nan sai mahukuntan wannan tsibiri suka nemi gwamnatin Amurka ta kama Bagudu, ta damka mata shi, domin a bincike shi dangane da rawar da ya taka wajen sato kudaden daga Najeriya zuwa tsibirin.
A lokacin kuwa Bagudu ya na Amurka zaune, ya ma shafe shekaru uku a birnin Texas.
Jami’an tsaron Amurka a Texas sun yi cacukui da Bagudu, suka tsare shi, daga nan aka garkame shi a kurkuku tsawon watanni shida.
Bayan tsare su, an ci gaba da binciken irin makudan kudaden da aka samu a cikin asusun wani kamfanin su mai Doraville Properties Corp. Bagudu da Mohammed ne masu kamfanin, kuma a asusun bankin Deutsche Bank International na Jersey suka kimshe kudaden.
Sai dai kuma kafin a dauke shi zuwa Tsibirin Jersey domin fuskantar hukunci, Bagudu ya sasanta da hukumar Amurka da Jersey, inda ya amince zai maida sama da “dala milyan 163 zuwa Najeriya, bisa sharadin zai koma Najeriya, maimakon mika shi ga mahukuntan Jersey.”
Duk wadannan bayanai suka cikin wasu takardun Kotun Gundumar Columbiya da aka yi tashin-tashinar shari’a cikin Janairu, 2019.
An yi shari’ar ce tsakanin Gwamnatin Amurka da kuma kadarorin dukiyar da aka kimshe cikin Asusun Doraville Properties da ke bankin Deutsche Bank, asusun ajiya mai lamba 80020796. Akwai dala milyan 287 a cikin asusun.
An dai shigar da karar ce inda aka nemi gwamnati ta kwace kudaden da ke cikin asusun ta hana kowa kai hannun sa a kan su.
An sako Bagudu wanda a yanzu shi ne gwamnan Jihar Kebbi, bayan a matsayin belin-talala aka bar shi dawo da shi Najeriya domin ya fuskanci shari’a.
Wasu hujjoji da aka samu daga Jersey da kuma kasar Switzerland, duk an aiko su Najeriya domin taimaka wa Ofishin Antoni Janar tattara hujjojin da kotu za ta rike wuyan Bagudu tamau.
Sai dai kuma tun bayan dawowar sa Najeriya, ba a kama shi an tambaye shi rawar da ya taka a lokacin harkallar satar kudaden da Abacha ya yi ba.
Maimakon haka, Bagudu ya tsaya takarar sau uku, kuma duk ya yi nasara.
Ya yi takarar sanata, ya yi nasara. Sannan ya yi takarar gwamnan Kebbi a 2015, ya samu kuma ya sake takara a 2019, ya zarce.
Duk kokarin da PREMIUM TIMES ta yi don jin ta bakin Gwamna Bagudu kafin a buga wannan labari, bai yiwu ba.
An buga wayar sa, bai dauka ba. An tura masa sakon tes, har yanzu bai maido amsa ba.
Haka shi ma Antoni Janar na Najeriya, kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, an tambaye shi batun Bagudu da batun kwafe-kwafen takardun shari’ar da aka gudanar a Amurka, amma duk bai bada amsa ba, ballantana a ji ta bakinn sa.