Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Amma ita cutar Corona Virus sabuwar cuta ce da ba a taba samun ta a jikin mutum ba.
Sakamakon bincike da aka yi game da cutar ya nuna cewa akan kamu da cutar ne ta hanyar yin muamula da dabbobi na gida da na daji.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Haka kuma idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Rahotani sun nuna cewa cutar ta yadu zuwa kasashen duniya 24.
Tambayoyi da Amsoshi
1. Shin ko Kwayoyin cutar za ta iya shigowa Najeriya?
Tabas cutar za ta iya shigowa Najeriya daga kasar Chana idan wani dan Najeriya ko kuma dan Chana dake dauke da cutar ya shigo Najeriya.
2. Akwai rade-radin cewa wai cutar ta bullo a Najeriya?
Babu wani da ya kamu da irin wannan cuta a kasar nan, babu rahotan bullowar cutar a Najeriya.
3. Wasu matakan hana shigowa da yaduwar cutar ne gwamnati ta dauka a kasar nan?
Tun da aka samu rahoton barkewar cutar a Kasar Chana da yaduwar ta zuwa wasu kasashe Hukumar NCDC ta maida hankali wajen wayar wa mutane kai game da cutar da yadda za a kiyaye. Ta hanyar bude wurare domin aika wa da marasa lafiya cikin gaggawa idan aka samu makamancin wannan cuta a jikin wani.
4. Shin ko akwai ingantattun wuraren gwajin wannan cuta a Najeriya?
Wajen gwajin cututtuka da hukumar NCDC ta kafa na dauke da kayan aiki na zamani domin gwajin wannan cutar.
Sannan hukumar ta bada lambar waya kamar haka 07032864444 da za a iya kira domin sanar da mahukunta game da cutar.
5. A ina ne aka bude asibitocin a kasar nan?
A yanzu haka NCDC na kokarin bude asibiti irin haka a babban birnin tarayya Abuja, bayan nan akwai asibitocin a jihohin Legas, Akwa-Ibom, Ribas, Enugu, Delta, Cross River da Kano.
6. Za a iya tafiya zuwa kasar Chana daga Najeriya a wannan lokaci?.
Gwamnatin Najeriya ba ta hana kowa shiga kasar nan daga Chana ba sai dai ta yi kira ga mau bukatar zuwa kasar da su dan dakata tukunna.
7. Wasu matakai ne ya kamata a dauka bayan an dawo daga kasar Chana?
Da zaran mutum ya dawo daga kasar Chana kamata ya yi ya killace kansa a gida na tsawon kwanaki 14 domin samun tabbacin ko ya kamu da cutar ko a’a.
8. Wasu Lambobin waya ne za a iya kira koda an kamu da cutar?
Za a iya kira NCDC a wadannan lambobbin waya0800-970000-10 ko kuma a aika da sakon SMS: 08099555577 ko kuma WhatsApp: 07087110839.
9. Menene alamun wannan cuta?
Alamun cutar corona virus sun hada da; matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan cutar ta ya yi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
10. Ya ake kamuwa da coron virus?
Ana iya kamuwa da corona virus ne ta hanyar cudanya da dabbobi sannan idan ana yawan zama kusa da wanda ke dauke da cutar.
Amma har yanzu ana gudanar da bincike domin samun tabbacin yadda kwayoyin cutar ke shiga jikin mutum.
11. Akwai maganin rigakafin cutar?
Babu.
12. Akwai maganin da za a iya sha domin a warke daga cutar?
Akwai magunguna da za a iya bai wa wanda ke dauke da cutar domin ya samu sauki, amma kuma fa sau an yi haka tun kafin ya yi tsanani.
13. Ana iya warkewa daga cutar?.
Rahotanin sun nuna cewa daga cikin mutane 100 din da suka kamu da cutar a kasar Chana 98 sun warke. Sannan cutar baya gaggawar yin ajalin mutum.
An kuma gano cewa da dama cikin mutanen da suka mutu sun gamu da ajalinsu ne saboda suna dauke da wani cutar a jikinsu kafin suka kamu da corona virus.
14. Shin ko za a iya kamuwa da cutar idan aka yi amfani da kaya ko kuma abincin da aka shigo da su daga kasar Chana?.
Har yanzu dai babu barazanar cewa idan aka yi amfani da kaya ko kuma idan aka ci abincin da aka shigo da su daga kasar Chana.
15 wasu matakai ne mutum zai iya dauke domin guje wa kamuwa da cutar.
1. Yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu.
2. A rika rufe hanci da baki idan za ayi tari ko atishawa.
3. A daina mai-maita amfani da tsuman da aka rufe baki ko hanci da shi a lokacin da aka yi tari ko atishawa.
4. A rage yawan zama kusa da wadanda suka kamu da cutar.
5. Idan an kamu da cutar yayin da mutum ke kasar Chana mutum zai iya yin amfani da takunkumin hana kamuwa da cutar domin hana yada cutar.
6. Kamata ya yi ma’aikatan asibiti su dunga yi taka tsan-tsan wajen kula da mutanen dake dauke da cutar domin guje wa kamuwa da cutar.
7. Matafiya daga kasar Chana zuwa Najeriya za su iya kiran wannan lambar waya 0800-970000-10 idan sun kamu da zazzabi bayan kwanaki 14 da dawowan su Najeriya daga kasar Chana.
16. Ma’aikatan kiwon lafiya za su iya kamuwa da cutar?.
Tabas ma’aikatan kiwon lafiya na daga cikin mutanen da suka fi saurin kamuwa da cutar saboda mua’amula da suke yi da marasa lafiya.
17. Shin akwai banbancin cutar corona virus da SARS?.
Duka cututtukan na kama da juna amma banbancin da ke tsakanin su shine a yadda ake kamuwa da cutar.
Bincke ya nuna cewa kwayoyin cutar SARS sun fi saurin shiga jikin mutum fiye da yadda cutar corona.
18. Gargadin WHO ga ksashen duniya game da cutar Corona Virus
WHO ta gargadi kasashen duniya da yi musu kira da su mai da hankali wajen kara inganta fannin kiwon lafiyar kasashen su.
Discussion about this post