Karamar Ministan Abuja Ramatu Aliyu ta bayyana cewa gwamnati za ta fara ciyar da yara abinci a makarantun firamare dake Abuja.
Ramatu ta sanar da haka ne a taron kaddamar da wannan shiri da aka yi a ‘Karu Model School’ a makon jiya.
Ta ce bisa ga tsarin shirin gwamnati za ta ciyar da yara 120,300 dake makarantun LEA 626 dake kananan hukumomi shida a Abuja.
“Gwamnati ta dauki ma’aikatan da za su girka abinci wa dalibai daga aji daya zuwa uku.
“ Shirin zai bukaci goyan bayan iyaye, malaman adinin, sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki da ma’aikatan da za su girkawa daliban abinci.
Ramatu ta kuma yi kira ga shugabanni, malaman addini da sarakunan gargajiya da su tallafa wa iyayen da basu da halin ciyar da ‘ya’yan su abinci musamman wanda zai inganta garkuwar jikin yaran.
Bayan haka ministan aiyukkan jinkai, agaji da inganta rayuwar al’umma Sadiya Farouq ta jinjina wa gwamnati bisa wannan shiri da ta kaddamar don ci gaban ilimi a babban birnin tarayyar.
Sadiya ta yi kira ga gwamnati da ta kara yawan kudaden abincin da ake biya akan ko wani yaro daga Naira 70 zuwa sama.
Idan ba a manta ba a shekarar 2016 ne gwamnati ta ware Naira biliyan 500 domin ciyar da yara dake makarantun firamare miliyan 24 a kasar nan.
Gwamnati ta tsara wannan shiri ne domin inganta ilimi, kawar da talauci tare da inganta kiwon lafiyar yara a kasan.