Zababben gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa da zarar ya dare kujeran mulki zai saka hannu a sabon tsarin biyan Albashi na naira 30,000 mafi kankantar Albashi a jihar.
Fintiri ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai bayan bayyana shi a matsayin sabon gwamnan jihar Adamawa.
A daren Alhamis ne babban Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe na Jihar Adamawa, Farfesa Andrew Haruna, ya bayyana sakamakon zaben da aka maimaita na kumfuna 44 a cikin kananan hukumomi 15 a jihar.
Da ya ke bayani, Haruna ya ce gaba daya Adamu Fintiri na PDP ya samu kuri’a 376,552.
Ya yi nasarar lashe zabe a kan abokin karawar sa, wanda ya zo na biyu, wato Gwamna Muhammadu Bindow na APC, wanda ya samu kuri’u 336,386.
Ya ce Sanata Abdul’aziz Nyako na ADC kuwa ya samu kuri’u 113,237, sai kuma Emmanuel Bello na SDP, ya samu kuri’u 29,792.
Fintiri ya rike Kakakin Majalisar Jihar Adamawa cikin 2014. Sannan kuma ya rike mukamin Gwamnan Riko cikin watan Yuli, 2014, bayan da aka tsige Gwamna Murtala Nyako na lokacin.
Gwamna Bindow na Adamawa, ya bi sahun takwaran sa na Bauchi, a jerin jihohin da PDP ta kwace daga hannun APC a Arewa masu Gabas Arewa PDP ta samu Sokoto, Adamawa, Bauchi, Benuwai, Taraba.
Akwai alamar PDP za ta iya kwace Kano daga hannun APC a kotu. Haka nan ma a jihar Zamfara, PDP na iya cin zabe a kotu, idan Kotun Koli ta soke zaben da aka bayyana nasarar APC.