Hukumar EFCC ta na shirin dakatar da shari’ar zargin wawurar kudade da ta key i wa tsohon Ministan Abuja, Bala Mohammed.
Hakan kuwa ya zama tilas, biyo bayan nasarar da Bala din ya samu ta lashe zaben gwamnan Jihar Bauchi da ya yi a karkashin jam’iyyar PDP.
Dokar Najeriya dai ta bai wa gwamna kariya, ta yadda wata hukuma ko kotu ba za ta tuhume shi ba, har sai bayan ya sauka daga mulki.
An zabi tsohon ministan Abuja, Bala, matsayin zababben gwamnan Bauchi a ranar 9 Ga Maris, inda ya kayar da gwamna mai ci a yanzu, Mohammed Abubakar na jam’iyyar PDP.
Tun bayan saukar Bala daga mukamin ministan Abuja cikin 2015, ya ke ta fama da kwaramniyar tuhuma da zargin wawurar kudade ta hanyar yin harkallar rabon filaye a Gundumar FCT.
Bayan an shafe wata da watanni ana binciken sa, an kama Bala can wajen karshen 2016, inda EFCC suka yi zargin sa da hannu wajen harkalla da badakalar filaye akalla na naira bilyan 1.6 a Abuja.
An kuma zarge shi da karbar rashawar naira milyan 550 domin ya mallaka wasu kadarori ga Aso Savings Limited.
An kuma zargi zababben gwamnan da karbar wasu naira milyan 314 daga Aso Savings Limited.
Daga nan kuma sai aka maka shi kotu, inda a karon farko tukunna aka fara tuhumar sa da zambar naira milyan 864.
A gaban Babban Mai Shari’a Abubakar Talban a Babbar Kotun Tarayya da ke Gudu, Abuja aka gurfanar da shi, a ranar 10 Ga Mayu, 2017.
An bayar da belin sa, inda kuma tun daga nan ba a sake kama shi ba, sai aka ci gaba da shari’a kai-tsaye.
Majiya da dama sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa akwai wasu binkice da dama da ake yi wa Bala, wadanda ba a ma kai ga gabatar da su a kotu a matsayin tuhuma ba tukunna.
Yayin da dokar Najeriya ta hana a gurfanar da gwamna a gaban kotu, sai dai kuma ba ta hana a ci gaba da bincike a kan zarge-zargen ba.
Dokar Najeriya Sashe na 308 na Kundin 1999, ya nuna cewa ba a gurfanar da gwamna a gaban kotu.
Sannan kuma Kakakin EFCC, Tony Orilade, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “ganin babu yadda za a yi a iya yanke wa Bala Mohammed hukunci kafin nan da ranar da za a rantsar da shi, wato 29 Ga Mayu, to daga ranar da aka rantsar da shi, ya shiga cikin rigar kariyar tuhuma kenan.”
Amma kuma EFCC ta ce sa waigi ga shari’ar Bala ba zai hana a ci gaba da shari’a da kuma tuhumar da ake yi wad an sa ba. domin Shugaban Kasa ne da Mataimakin sa, sai kuma Gwamna da Mataimakin sa kadai ne ke da rigar kariya.
Takardun tuhuma da ke a gaban kotu na zargin dan Bala Mohammed da harkallar naira bilyan 1.1, wadda aka ce ya wawura ta hanyar yin amfani da wasu kamfanonin ayyukan fasaha da na harkar noman zamani na gare.
Lauyan Bala mai suna Uche, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa duk zarge-zargen da ake yi wa Bala ba gaskia ba ne, siyasa ce da kuma bi-ta-da-kulli kawai, saboda ya na cikin wadanda suka yi gwamnati tare da Goodluck Jonathan.
Idan Bala ya sake cin zabe a 2013, to kuma tilas a sake dage shari’ar sai nan da shekara takwas za a iya ci gaba kenan.