Gwamnonin jam’iyyar APC su 24, sun amince da Shugaba Muhammadu Buhari ya fito takarar shugabancin kasa karo na biyu a karkashin tutar jam’iyyar a zaben 2019.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Rochas Okorocha na jihar Imo ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnatin tarayya jiya bayan kammala ganawar da suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari.
A ta bakin Okorocha, gwamnonin 24, wadanda 17 daga cikin su duk tsoffin ‘yan jam’iyyar PDP ne, sun shaida wa Buhari wannan goyon baya na su a ganawar da suka yi da shi.
Ya ce sun je ne domin su jaddada masa goyon bayan su, kuma su nuna masa wajibcin sa na sake tsayawa takara domin ya ci gaba da jidalin ceto kasar nan da ya ke yi daga halin da aka jefa ta a baya.
“Mun kuma tattauna batun taron gangamin jam’iyya da za a gudanar da kuma batun zaben shugaban jam’iyya, inda muka tabbatar masa da cewa za mu zabi shugaba nagari wanda ya goge wajen iya tafiyar da jama’a a cikin tafiyar siyasa.
“Mun kuma shaida masa cewa ba za mu taba yarda batun ‘yan takara da yawa ya damalmala mana jam’iyya ba.
Okorocha ya musanta zargin da ake yi cewa sun yi ganawar ce da Buhari domin su mara wa Adams Oshimhole baya ya zama shugaban APC.
A na sa jawabin, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa shugaban jam’iyya a kananan hukumomi da mazabu duk za su kasance ne sun fito babu hamayya, ta hanyar cimma daidaito a tsakanin juna.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da: Nasir El-Rufai, Yahaya Bello, Simon Lalung, Jubrila Bindow da Abdulaziz Yari.
Sauran sun hada da Rochas Okorocha, Abdulahi Ganduje, Kashim Shettima, Abubakar Sani Bello, Tanko Almakura, Abiola Ajimobi, Ibikunle Amosun, Godwin Obaseki da Abubakar Badaru.