Gwamnan Jihar Kaduna Nasir wadanda aka fi sani da CJTF a fadin kananan hukumomini 23 na jihar.
Gwamnatin Jihar ta ce an maye gurbin su da sabbin jami’an tsaron sa kai da gwamnatin jihar ta kaddamar a garin Kaduna, wadanda su ne ke taimakon ‘yan sanda wajen fuskantar kalubalen dakile aikata laifuka a cikin al’ummar fadin jihar.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wurin kaddamar da ‘yan bijilante a Kaduna.
Gwamnan wanda mataimakin sa Barnabas Bantex ya wakilta, ya kara jaddada aniyar gwamnatin jihar wajen kakkabe laifuka da miyagu a fadin jihar.
Daga nan sai ya y i kira da a ba sabbin ‘yan bijilante din hadin kai da goyon baya. Ya kuma yi kira ga ‘yan CJTF da aka soke da su gaggauta shiga aikin sabon bijilante din da gwamnati ta amince dashi.