Yayin da ‘yan Najeriya a fadin kasar nan ke fama da matsalar karanci da tsadar man fetur, a ko’ina cikin adin kasar nan, akwai alamomin da ke nuni da cewa karancin fetur zai kara kamari nan ba da dadewa ba.
Hujjar fadin haka kuwa ta biyo bayan gargadin kwanaki 14 da kungiyar masu daffo-daffo na ajiye man fetur su ka bayar cewa idan ba a biya su bashin da su ke bi na naira bilyan 650 ba, to za su tafi yajin aikin-sai-an-bya-mu kudin mu. PREMIUM TIMES HAUSA ta bi diddigin matsalar man fetur, domin gano shin da wace hujja ce ake dora wa gwamnatin Buhammadu Buhari laifin wannan halin kuncin da ake ciki?
ASALIN MATSALA:
1 – Za a iya cewa wannan matsala ta samo asali ne, tun bayan saukar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo daga mulki, cikin 2007.
2 – Yayin da marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua ya hau mulki, ya gaji farashin litar man fetur a kan naira 75 da Gwamnatin Obasanjo.
3 – Maimakon Umaru ya kara kudi, kamar yadda gwamnatocin baya su ka rika yi, sai ma ya rage kudin, daga N75 zuwa naira N65. Hakan ya sa an rika jinjina masa har bayan babu ran sa.
4 – Goodluck Jonathan ne aka wayi gari a ranar 1 Ga Janairu, 2012, a jawabin san a sabuwar shekara ya yi wa al’ummar kasar nan albishir da karin kudin mai daga N65 zuwa N141, wato karin naira 76 kenan a kowace lita.
5 – Jonathan ya hadu da fushin ‘yan Najeiya, musamman kungiyoyin kwadago, daliban jami’o’i, masu rajin kare jama’a da kuma ‘yan adawar siyasa.
6 – An yi ta yajin aiki, da zanga-zanga a kasa baki daya, har dai harkokin gwamnati suka gurgunce, a karshe, Jonathan ya maida farashi naira 97, aka hakura.
7 -Tallafin mai ne gwamnatin Jonathan ta ce ta janye, abin daya haifar da rudu kenan.
8 – Muhammadu Buhari na a sahun gaba wajen gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da karin kudin mai. Baya ga zanga-zangar da ya fito, har ikirari ya yi cewa ko naira 50 dan Najeriya ya sha litar man fetur, to an zalunce shi.
9 – Goodluck Jonathan ya rage farashin litar man fetur daga 97 zuwa 87, cikin watan Faburairu, 2015. Sai dai wannan rangwame bai yi wani tasiri ba, domin an rika kallon saboda zabe ne ya yi ragin, ba don tausayin jama’a ba. An yi ragin ne ana saura wata daya zaben shugaban kasa.
10 – Hawan Gwamnatin APC, ta fuskanci gagarimar matsalar man fetur, ta yadda aka yi wa lita daya gwauron kari, daga N87 zuwa 148. Daga baya aka rage naira uku, ya koma 145.
11 – Tashin farashin dalar Amurka, da faduwar darajar farashin gangar danyen man fetur, na daga cikin abin da ya haifar da matsala.
12 – Sai dai kuma an dora wa gwamnatin Muhammdu Buhari wannan laifi, domin ya yi wa jama’a alkawarin cewa da ya hau mulki, zai maida dalar Amurka farashi daya da naira. Sannan kuma zai rage litar mai daga naira 87 zuwa naira 45.
13 – Maimakon haka, sai naira ta ki saukowa kuma ka maida lita daya naira 145.
14 – Farkon watan Disamba, 2017, an rika buga rahotannin cewa za a fuskanci matsalar mai, amma gwamnati da NNPC su na karyatawa.
15 – Kafin Kirsitime kasar nan ta dume da matsanancin karancin mai, har ta kai ana saida lita daya naira 300. Har yau kuma matsalar na nan ana fama da ita.
16 – A zaman yanzu, tun kafin Kirsimeti, kamfanoni masu zaman kansu bas i iya daukar dala su fita su sayo fetur, domin faduwa za su yi, saboda dala ta yi tsadar gaske.
17 – NNPC ce kadai ke iya sayo mai daga waje, ita kuma ta ce a yanzu farashin dakon man da saukalen sa a Nijeriya ya karu, duk lita daya ta na kama mata a kan 171, daga saye zuwa saukewa.
18 – NNPC na ta yin baki-biyu. A gefe daya ta na cewa ba za ta kara kudin mai ba. A daya gefe kuma ta na cewa ita ma ba za ta iya juri zuwa kasuwa ta sayo mai ya na kama mata naira 171, amma ta na saidawa 145 ba. Sannan kuma har yau ba a tace mai a kasar nan, duk da alkawarin da APC ta yi cewa da ta hau za ta gyara matatun bai domin a huta da sayowa a kasashen waje.
19 – A yanzu kuma ga kungiyar masu daffo-daffo sun ce su na bin gwamnati naira bilyan 650, kudin da ya kamata NNPC ta rika rangwanta musu idan sun sayi mai.
20 – Tunda babu alamar za a iya biyan su wannan makudan kudade, akwai kwakkwaran dalilin su kenan na tafiya yajin aiki.
Shin APC ta kawo waraka a harkar mai, ko kuwa dagula harkar ta kara yi?
TARIHIN KARIN KUDIN FETUR A NAJERIYA
• Gowon – daga 6k zuwa 8.45kobo
• Murtala – daga 8.45k zuwa 9k
• Obasanjo – daga 9k zuwa 15.3k
• Shagari – daga 15.3k zuwa 20k
• Buhari – daga 20k to 20k (bai kara ba a wancan mulkin sa).
• Babangida – daga 20k zuwa 39.5k
• Babangida – daga 39.5k zuwa 42k
• Babangida – daga 42k zuwa 60k (kari kan motocin da ba na haya ba).
• Babangida – daga 60k zuwa 70k
• Shonekan – daga 70k zuwa N5 (Naira)
• Abacha – daga N5 zuwa N3.25k (ya rage farashi).
• Abacha – daga N3.25k zuwa N15
• Abacha – daga N15 zuwa N11 (ya rage farshi).
• Addulsalami – daga N11 zuwa N25.
• Abdulsalami – daga N25 zuwa N20 (ya rage farshi).
• Obasanjo – daga N20 zuwa N30
• Obasanjo – daga N30 zuwa N22 (ya rage farashi).
• Obasanjo – daga N22 zuwa N26.
• Obasanjo – daga N26 zuwa N42.
• Obasanjo – daga N42 zuwa N50.
• Obasanjo – daga N50 zuwa N65.
• Obasanjo – daga N65 zuwa N75.
• Yar’Adua – daga N75 zuwa N65 (ya rage farshi).
• Jonathan – daga N65 zuwa N141.
• Jonathan – daga N141 zuwa N97.
• Jonathan – daga N97 zuwa N87.
. Buhari – daga N87 zuwa N145
Discussion about this post