Siyasar jihar Kaduna ta damalmale cikin rudani, zargi da rashin natsuwa musamman a ‘yan kwanankinnan.
Masu sharhi kan siyasa suna ganin hado kan ‘yan siyasan Kaduna musamman na jam’iyyar APC, abu ne mai dan Karen wuye.
Dama can ba zaman lafiya a keyi tsakanin sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, sanata Shehu da gwamanan jihar ba Nasir El-Rufai kwanaki kadan bayan an rantsar da su kujerun mulki.
Kowa yana nuna shine mai gaskiya sannan jagoran talakawa a jihar.
Sanata Shehu Sani ba boyayye bane a labban mutanen jihar Kaduna, kai ba ma Kaduna ba duk Kasa ne baki daya. Da yake dama can gogaggen dan kare hakkin dan Adam ne, shiga siyasa bata zama masa sabuwa ba. Sai dai tun da ya dare kujerar sanata a majalisar dattawa, shi da gwamnan jihar Kaduna suka fara zaman doya da manja. Ba a ga mai maciji a tsakanin su.
Sau dayawa sun sha kai ruwa rana tsakanin sa da gwamna El-Rufai inda ya ke sukan gwamnan da rashin iya gudanar da mulki a jihar ba.
A haka dai ana ta tafiya, har gashi a makon nan ne gwamna El-Rufai ya maka Sanata Shehu Sani a kotu wai don yana bata masa suna.
Ba da dadewa ba, sanata Shehu ya maida wa El-Rufai martane cewa a shirye yake da dambata a kotu. Cewa ai mai tsoron zafi ba zai kai kan sa dakin girki ba.
A haka dai tuni aka ja daga, kowa ya wasa wukar sa.
Shi ko Sanata Suleiman Hunkuyi, salon damben nasa da gwamnan El-Rufai da bam ne. Tun farko dai Hunkuyi na daga cikin ‘yan lelen gwamna El-Rufai, Komai dashi ake yi sannan babu abin da yakan nema a gwamnati ba ayi masa, kamar yadda masu sharhi suka zayyana.
Sule Hunkuyi sun fara samun matsalane da gwamna El-Rufai tun bayan zaben deliget da akayi na jam’iyyar inda suka zargi gwamnan da hana kowa sa baki a zaben, wato sai yadda yaso. Hunkuyi, Shehu Sani da wasu jigajigan ‘yan jam’iyyar sun nuna bacin ransu kan haka.
Tun daga wannna lokaci fa El-Rufai da Hunkuyi suka sa kafar wando daya.
Abin dai kamar za a shirya ga shi har ya kai ga maganan shiri ya sha ruwa.
A makon da ya gaba ta ne gwamna El-Rufai ya umurci hukumar tsara gari da yanayin kasa KASUPDA su rusa ofishin jam’iyyar APC bangaren Hunkuyi a Kaduna.
Hakan dai ya jawo cece-kuce game da abin da ya faru, inda wasu suke cewa abin da akayi ba daidai bane. Sai dai kuma gwamnatin jihar ta ce tayi haka ganin cewa wannan gida fa ba a biya mata kudin harajin kasa.
Bayan haka an sake tura masa takardu ya biya kudin harajin kasa na gidan sa dake Inuwa wada nan da kwanaki 30 ko ya fuskanci fushin KASUPDA.
Duk da abubuwan da ke faruwa a siyasan ce a jihar Kaduna, mutanen jihar da yawa suna ganin El-Rufai ya fisu gaskiya.
Bayanai da mutanen jihar suka yi shine, gwamnan dai yana aiki domin gyara jihar wanda shine makasudin zaben sa da akayi. Suna ganin babu abin da zai hana su sake zaban sa idan yace zai sake takara a jihar Kaduna.
Wannan zance ne na wasu bangare, wasu kuwa suna ganin fadar gwamnan jihar El-Rufai, ta yi masa yawa. Wasu na ganin sarkin Yawa yafi sarkin Karfi. Idan suka taru dukkan su za su kada shi a zabe mai zuwa.
Kalubalen kuwa shine, waye cikin su zai yarda ya bi wani don samun nasara kan haka, sannan wani dan takarane zai ja da shi gwamna mai ci da dai sauran su.
Lokaci ne kawai ake jira.
Discussion about this post