Oyegun ya amsa wasikar Tinubu

0

Shugaban jam’iyyar APC John Oyegun ya rubuta wa Jagorar jam’iyyar APC Bola Tinubu wasika don bashi amsar wasikar da ya rubuta masa ya na zargin sa da yi masa zangon Kasa a aikin sasanta rikicin da ya dabaibaye ‘ya’yan jam’iyyar a jihohin kasar nan.

Sai dai kuma maimakon ya amsa korafe-korafen da Tinubu ya zayyano a cikin wasikar sa Oyegun ya bige da yi wa Tinubu fatan Alkhairi ne kan aikin sasanta rikicin jam’iyyar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa shi ya yi.

” Ina yi wa Tinubu fatan alkahiri kan abi da ya sa a gaba na seta mana jam’iyya da ‘ya’yan jam’iyyar mu.

” Duk abin da ya ke nema daga gare mu a jam’iyya, zamu bashi na taimako domin sanin nasara a aikin da ya sa a gaba.

Share.

game da Author