Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum ya nuna rashin jin dadin kan yadda Sojoji ke tunkarar yaki da Boko Haram a jihar Barno.
Gwamna Zulum ya ce lallai akwai sake kan yadda sojoji ke aikin kakkabe Boko Haram a jihar.
Idan ba a manta ba Gwamna ya tsallake rijiya da baya daga harin kwantar baunar Boko Haram a hanyar sa ta dawowa garin Maiduguri daga kananan hukumomin Monguno da baga.
Gwamnan Zulum ya ziyarci kananan hukumomin Monguno da Baga wajen rabawa mazauna sansanonin ‘yan gudun hijra kayan abinci.
Mjiya masu karfi da suka tabbatarwa PREMIUM TIMES, aukuwar wannan al’amari sun shaida cewa sojoji da ‘yan sandan dake gadin gwamna Zulum ne suka yi artabu da ‘Yan Boko Haram din har gwamna Zulum ya tsallake wannan hari.
Baya ga gwamna Zulum, wasu ma’aikatan hukumar bada agaji na jihar, sun afka wairin wannan tarko na Boko Haram.
Shugaban hukumar ta tabbatarwa PREMIUM TIMES da haka sai dai bata bada wani karin bayani a kai ba.
A lokacin da yake tattaunawa da kwamandan Sojojin Kasa dake aikin samar da tsaro a yankin Baga, anji gwamnan na cewa bai gamsu da yadda sojojin suke tunkarar yakin ba. Sai dai kuma shi kwamandan dake tsaye a gefe ya yi kokarin wanke sojojin cewa su ne suka fatattake su kuma yana tabbatar masa cewa babu Boko Haram koda mutum daya ne a garin Baga.
Kakakin rundunar Soji, Sagir Musa, ya shaida cewa ana nan an gudanar da bincike mai zurfi akan abin da ya faru da kuma shirya wasu dabaru da za aafka wa Boko Haram.