Jim kadan bayan sauko wa daga sallar Idi shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da manema labarai a fadar shugaban kasa inda a nan ne yayi sallar Idi tare da Iyalansa.
Buhari ya shaida wa ‘yan ksa irin hubbasan da gwamnatin sa ta yi wajen kakkabe Boko Haram a yankin Arewa mMaso Gabas.
” Mun samu nasarorin ganke a fannin tsaron kasar nan fiye da yadda muka gada a 2015. Amma duk da haka akwai sauran aiki a a gaban mu musamman a yankin Arewa Maso, Yamma da Arewa Ta Tsakiya.
Buhari ya kara da cewa gwamnatin sa za ta samar wa fannin tsaro karin kudade masu yawa domin tunkarar yan ta’adda da suka hana mutanen kasa zaman lafiya.
Game da manyan hafsoshin Kasar nan kuma, mun zura musu ido domin ganin sun kara kaimi bisa aikin samar da zaman lafiya a yankunan da ta’addanci yayi tsanani a kasar nan.
Sannan kuma Shugaban Buhari ya gargadi ‘Yan tsageran yankin Neja-Delta masu fasa bututun mai, cewa su daina hakan.
” Idan suka fasa bututun mai zai latata ruwan dake gudana a yankin. Hakan zai hana mutanen yankin da masunta ne. Kafin ‘yan Najeriya su jigata sai ‘yan yankin sun jigata.
A karshe shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da maida hankali wajen gano barayin gwamnati sannan da hukunta su kamar yadda dokar kasa ta gindaya.
Discussion about this post