KIRA GA MATASA: Ku daina rudin kanku cewa Korona ba ta kama matasa, har kisa ta na yi – Shugaban WHO

0

Shugaban Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus ya gargadi matasa da ke cewa kwayoyin cutar Korona ba zai iya kama su ba da su daina wannan zato, yana mai cewa ba kama matashi ba ma kawai har kisan sa zai iya yi idan bai kiyaye ba.

Bayan haka kuma ya shaida cewa lokaci yayi da kasashen duniya za su koyi shirin zama dindindin da kwayoyin tutar Korona.

“Dole ne mu koyi rayuwa da wannan cuta tare da ɗaukar matakai domin mu rayu, tare da kare kanmu da sauran jama’a.”

Sannan kuma ya yabawa kasar Saudiyya kan irin matakan da ta ɗauka yayin gudanar da Aikin Hajjin bana.

Hotuna da suka fito daga can kasar ya nuna yadda mahukunta suka yi tsari yadda mutane za su yi aikin Haji cikin natsuwa, kariya da nesanta da juna domin Korona.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 481 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -89, FCT-96, Filato-68, Ogun-49, Edo-44, Rivers-43, Oyo-25, Osun-23,Delta-15, Enugu-11, Kano-7, Kaduna-7, Bauchi-2, Bayelsa-1 da Yobe-1

Yanzu mutum 42,689 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 19,270 sun warke, 878 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,541 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,043 FCT – 3,710, Oyo – 2,713, Edo – 2,285, Delta – 1,501, Rivers 1,782, Kano –1,591, Ogun – 1,385, Kaduna – 1,403, Katsina –742, Ondo – 1,123 , Borno –613, Gombe – 607, Bauchi – 541, Ebonyi – 785, Filato – 1,124, Enugu – 801, Abia – 545, Imo – 468, Jigawa – 322, Kwara – 753, Bayelsa – 328, Nasarawa – 312, Osun – 523, Sokoto – 153, Niger – 224, Akwa Ibom – 221, Benue – 346, Adamawa – 140, Anambra – 135, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 66, Ekiti – 132, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 45.

Share.

game da Author