Zan bayyana dalilin da ya sa na yi hannun riga da Kwankwaso – Shugaban PDP na jihar Kano, Bichi

0

Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Kano, Rabiu Sulaiman-Bichi, ya canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Bichi wanda daya daga cikin nagaban goshin tsohon gwamnan jihar Kano ne, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai bayyana ainihin dalilan da ya sa ya fice daga jam’iyyar PDP duk da Rabiu Kwankwaso na cikin ta.

Idan ba a manta ba Jam’iyyar PDP ta fadi kasa warwas a hukuncin kotun koli da aka yanke a karshen wannan mako. Kotun Koli ta tabbatar wa APC da kujerar gwamna na jihar Kano.

Bichi ya taba zama shugaban humar raya birane na jihar Kano, sannan ya rike kujerar sakataren gwamnatin jihar Kano duk a karkashin gwamnatin Kwankwaso.

Sannan kuma shine babban jami’i da ya kula da zaben gwamna na jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Share.

game da Author