An karrama DPO Francis Erhabor, na Karamar Hukumar Itam, cikin Jihar Akwa Ibom, bisa dalilin cewa bai taba karbar cin hanci ko toshiyar baki ba, tun daga ranar da ya fara aikin dan sanda.
“Tun daga ranar da na fara aikin dan sanda ban taba karbar toshiyar baki ba.
Na shiga aikin nan a lokacin da wannan aiki ya yi matukar baci da cin hanci.
“Amma sai na raya a rai na cewa, ‘ya ubangiji, idan har na kuskura na karbi cin hanci ko ma na naira nawa ne a yayin aikin nan, to kada ka rufa min asiri.
Ubangiji ka tozarta ni, ka wulakanta ni, a rika nuna ni a NTA, BBC da CNN a matsayin wulakantacce.” Haka Erhabor ya bayyana kwanan nan.
Ya kara da cewa duk wanda ya san ya taba karbar ko da cin hancin naira 20 ne, to ya fito ya tozarta shi gaban jama’a.
An karrama Erhabor a Abuja, ranar Litinin da ta gabata, tare da wasu mutane biyar.
Kungiyar bada kyautar cancanta ga mutane nagari, wato, Integrity Icon Award Summit ce ta karrama su.
Wannan kungiya, gambiza ce tsakanin Accountability Lab, Luminate MacArthur da Ford Foundation, domin zakulo wasu ‘yan Najeriya masu gaskiya a cikin ma’aikatan gwamnati.
Sauran biyar din da aka karrama sun hada da Tani Nimlan ta NAFDAC, Christian Ahiauzu na ICT a Jami’ar Fatakwal, Tina Odinakachi, malama a Jami’ar Jos, da kuma Kacheilom Robert-Ndukwe, wani malamin sakandare a jihar Ribas.
Erhabor ya bayyana cewa tun sama da shekaru 30 da suka gabata ya shiga aikin dan sanda, amma har yau bai taba karbar cin hanci ba.
“An dauke ni aikin dan sanda a matsayin ‘Cadet Inspector’ a ranar 2 Ga Afrilu, 1990. A lokacin shekaru na ba su wuce 17 da wasu watanni a duniya ba.”
Ya ce babu irin kalubalen da bai fuskanta a rayuwa ba, amma har yau bai yarda ya bi son ran sa ko son abin da ya kauce wa shari’a ba.