Boko Haram sun kashe sojoji 8, sun raunata 5

0

Boko Haram sun kashe wani babban jami’in sojan Najeriya da kuma wasu kananan sojoji bakwai, a wani harin kwanton-bauna da suka kai wa sojojin a llokacin da suke sintiri.

An kuma tabbatar da an jikkata wasu sojojin biyar, sannan kuma wasu biyu har yau ba a san inda suke ba, bayan al’amarin da ya afku jiya Talata.

Majiya ta kara da cewa an kashe dan Boko Haram daya, an kuma kwace bindigar da ke hannun sa.

An dai kai wa sojojin na Bataliya ta 156 hari misalin karfe 1:00 na rana a Mainok, wani kauye da ke nisan kilomita 60 tsakanin sa da Maiduguri.

Sojoji sun kwaso gawarwakin wadanda aka kashe, tare kuma da wadanda aka jikkata din.

An garzaya da wadanda suka ji rauni a wani asibitin sojoji kamar yadda majiyar PREMIUM TIMES ta tabbatar.

An kuma rasa inda aka yi da wasu motocin harba iggwa guda biyu da kuma makamin harbo jiragen yaki guda uku duk sun bace, an rasa inda suke bayan harin wanda Boko Haram suka kai wa sojoji.

An kasa tabbatar da shin Boko Haram ne suka yi awon-gaba da su, ko kuwa sojoji ne suka sauya musu mabuya.

Da safiyar yau PREMIUM TIMES ta kira kakakin sojojin Najeriya, Sagir Musa domin jin ta bakin sa, amma bai dauki waya ba.

Bayan sun yi shiru na wasu ‘yan makonni, yanzu kuma Boko Haram sun sake yunkurowa da karfin su cikin kwanakin nan.

Sun kara kaimi har ta kai su na ci gaba da kai hare-hare a kan fararen hula da tare babban titin shiga Maiduguri da ga Damaturu, wanda shi ne kadai hanyar da ake iya shiga babban birnin na jihar Barno.

Share.

game da Author