Gwamnatin Buhari na neman jefa Najeriya cikin rami gaba dubu – Obasanjo

0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na kokakin jefa Najeriya cikin rami gaba dubu na bala’i da rashin kwanciyar hankali.

Obasanjo ya yi wannan furuci ne a wata tattaunawa ta musamman da PREMIUM TIMES a gidan sa da ke Ibogun Olaogun, cikin Karamar Hukumar Ife, a Jihar Ogun.

An yi wannan tattaunawa ce a cikin watan da ya gabata.

Tattaunawar ta na cikin wata Mujalla ta Musamman da PREMIUM TIMES ta buga domin cikar Najeriya shekaru 20 bayan dawowar mulkin dimokradiyya, tun daga 1999.

Da ya ke bayani, Obasanjo ya ce Najeriya ta samu ci gaba bakin gwargwado a karkashin mulkin PDP daga 1999.

Sai dai kuma ya ce a bisa la’akari da yadda kasar ke tafiya a yanzu, to Najeriya na neman fadawa rami gaba dubu.

“Surutan da ake ta yi wai ana ci gaba a yanzu, duk tatsuniya ce. Shin da sauri ake ci gaban ko da tafiyar-hawainiya? Shin gaba ake ci ko kuwa tafiyar kura ake yi? Shin kwan-gaba-kwan-baya ake yi, ko kuwa tafiya ake yi ana sakin hanya?

“Mutum zai rika yin wadannan tambayoyin, amma fa ba mu da wani zabi sai mun fi hanya madaidaiciya sannan za mu iya kai gaci. To yanayin yadda mu ke tafiya a yanzu, kasar nan ta kama hanyar afkawa rami gaba dubu.”

Da ya juya a kan tattalinn arziki, Obasanjo ya ce babu wani abu da aka tsinana a yanzu.

Ya ci daba da cewa ci bagan da aka samu din ma a baya, duk an yi sakaci a yanzu ya shiririce.

Da aka tamabaye shi abin da ya haifar da haka, sai Obasanjo ya ce saboda a yanzu Najeriya an ki yin abin da ya dace domin a jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na waje.

Ya kara da cewa harankazamar da ake yi da sunan inganta tattalin arziki ya haifar da halin rashin tabbas din da tattalin arzikin ke ciki.

Duk da cewa Najeriya ta fita aga cikin halin matsin tattalin arzikin da ta afka cikin 2016, gwamnati na ikirarin cewa an fita daga kuncin.

Sai dai kuma har zuwa yau maimakon a ga sassauci, sai hauhawar yawan masara aikin yi ake adin kasar nan.

‘Shirin Yaki da Rashawa Ya Gurbace’

Obasanjo ya ce shirin yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnatin ke yi, tuni ya gurbace, ya zama shirin cin rashawa shi kan sa.

Daga nan sai ya ce a lokacin da ya fito da shirin hana cin hanci da rashawa, 1999 zuwa 2007, dukkan alkawurran da ya dauka babu wanda bai cika ba, ciki har da yaki da cin rashawa din.

“Tun da na kafa ICPC da kuma EFCC, na bar su sun rika cin gashin kan su, ba na yi musu katsalandan. Kuma ban taba cewa ICPC ko EFCC “ku kama wane ba.”

Obasanjo ya kara da cewa a lokacin mulkin soja, duniya ta maida Najeriya saniyar-ware, har aka kore da daga Kungiyar Kasashe Rainon Ingila.

“Amma cikin shekarun mulki na a zangon farko na 1999 zuwa 2003, sai da aka maida Najeriya cikin kungiyar, domin martabar kasar ta dawo a idon duniya. Har ma mu ka dauki nauyin taron Kungiyar Kasashe Rainon Ingila din wato, Commonwealth.”

“Ba zan taba mantawa ba akwai ranar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya a lokacin mulki na, Charles Soludo ya ce min “Ranka ya dade, a cikin mako daya muka samu dala milyan 80. Ba fa daga kudin fetur ko cocoa ba. Daga kudaden da ke shigowa daga kasashen waje kai tsaye.

“Na ce masa ni abin da na ke so mu rika samun dala milyan 100 a kowace ranar aiki. Wato dala milyan 500 kenan a mako daya, banda ranakun Asabar da Lahadi. A shekarar a samu dala bilyan 26 kenan,”

A yanzu kuma ya nuna damuwa dangane da yanayin tsarin gwamnati, wanda ya ce bangaranci na ci gaba da kunno kai a ciki.

“Yanzu mun tsinci kan mu inda za a samu manyan shugabannin bangarorin gwamnatin tarayya uku duk daga Arewacin kasar nan (Wato Buhari, Sanata Ahmed Lawan da Cif Jojin Najeriya). Shin ta yaya za a kafa gwamnati haka a ce kuma babu wani abin damuwa?

Daga nan ya ce kamata ya yi a yi wa Dokar Mulkin Najeriya gyara, domin kauce wa irin wannan badambadama.

Share.

game da Author