Alaka Tsakanin Rashin Ilmi, Rashin Aiki Da Matsalar Tsaro A Najeriya Musamman A Arewacin Nageriya, Daga Kais Sallau

0

Matsalar tsaro abune wanda yayi katutu a Najeriya musamman arewacin Nageriya wanda ya hada da rikicin kabilanci, masu garkuwa da mutane, yan bindiga dadi, masu satar sanu da sauransu.

Haka kuma arewacin Najeriya na fama da matsalar rashin ilmi inda a binciken (UNICEF) da sukayi na 2018 ya nuna cewa kashi sittin da tara (69%) na yaran da basu zuwa makaranta a Nageriya daga arewacin Najeriya suka fito. Hakan ya samo asali ne sakamakon rashin kulawa daga iyayen yaran da sakarcin gwamnati.

Haka a farnin aikin yi, idan ka duba kididdigar da sashin kididdiga na kasa (NBS) ta fitar a binciken da tayi 2018, zamuga cewa kashi ashirin da uku da digo daya (23.1) na yan Najeriya basu da aikin yi wanda akarinsu matasa ne kuma daga arewacin Nageriya. Haka kuma masu aikin akasarinsu abinda suke samu bai taka kara ya karye ba.

Rashin aikin da ya addabi matasa a arewacin Najeriya ya samu asali ne daga rashin kishi da son zuciyar masu mulki ne musamman manyan arewa da kuma rufe masana’antun arewacin Nageriya da akayi.

Akasarin masu mulki na arewa ba damuwansu bane su kirkiro hanyar da zasu samarwa matasa da aiki tunda sunsan yaransu basu samun matsala gurin samun aiki. A kullum burinsu su tara kudi kawai, sun manta cewa duk lokacin da rashin aiki yayi yawa a guri, toh dole ayi fama da rashin kudu, idan kuma mutane na fama da rashin kudi, toh sai kariyar Allah.

Sannan rufe masana’antun arewacin Najeriya da akayi, shima ya taimaka gurin matsalar rashin aiki a Arewa. Saboda mutane dayawa sun rasa ayyukansu sanadiyar rufe su. Gwamnati bazata iya bawa dukan yan kasa aiki ba, amma to hanyan gayyato yan kasuwa da wadansu kasashe su kafa masana’antu zasu samarwa matasa dayawa aiki. Akasarin kasashen da suka ci gaba mafi yawan yan kasan ba aikin gwamnati suke yi ba, a masana’antun masu zaman kansu suke aiki.

Alaka Tsakanin Rashin Ilmi Da Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya

Ba shakka matsalar ilmi na daya daga cikin abinda ya taimaka gurin fadawar arewacin Nageriya halin matsalar tsaro. Kama daga ilmin addini zuwa ga ilmin boko. Daga binciken da (UNICEF) sukayi zamu fahimci cewa yara da yawa basu zuwa makaranta wanda dayawa daga cikin su laifin iyayensu da kuma gwamnati musamman gwamnonin arewa.

Kusan a kowace jihar a arewacin Nageriya zaka samu makarantar primary school kyauta ne, secondary school kuma idan na gwamnati ne zakaga kudin makarantar ba wani yawa yake dashi ba. Sai kudin rubuta jarabawan gama secondary shi ke da yawa wanda da izni Allah shima bazai gagara ba.

Amma zaka ga mutum ya haifi yaro bai kaishi makarantar addini ba, bai kuma sashi a makarantar boko ba. Saidai kaga yaro a bola wai yana tsintar bola. Toh yaro ya saba da bin bola yana tsintar kaya, yana samun naira dari uku (300) a rana, sai ga wani yace mishi suje su sace mutum ko suje su sace shanu zai samu dubu dari biyu (200,000) a rana daya. Toh mai kake tsammani, idan ba wanda Allah ya kiyaye ba, tafiya zai yi, domin baida Ilmi da zaiyi tunanin cewa, wannan abin fa zulunci ne, kuma zaluntar wani a addinimu haramu ne.

Toh, ta yaya kake tunanin wanda baida Ilmi zai ji tausayin musgunawa wani ko zaluntar wani tunda ba addinin ya sani ba. Bazamu ce baa samun masu Ilmi wadanda suke shigan miyagun aiki ba, amma dayawansu basu samu Ilmi ba. Naga wani shugaban masu garkuwa da mutane na hanyan Kaduna zuwa Abuja da yan sanda (Police) suka kamasa, yace musu “shi bai taba yin karatun addini ko boko ba. Kuma dayawansu haka suke”. Hakan ya samo asali ne na rashin kulawa da fulani da gwamnati suka yi gurin Ilmi. Ya kamata ace akwai tsarin da gwamnonin arewa suka fito dashi domin ba fulani makiyaya ilmi.

Alaka Tsakanin Rashin Aiki Da Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya

Matsalar rashin aiki na daya daga cikin abinda ya taimaka gurin yawaitar matsalar tsaro a arewacin Nageriya. Duk gurin da akace mutane na fama da rashin aiki, toh ba shakka sai anyi fama da rashin kudi a wannan gurin.

Duk dan adam yana da bukatunsa na yau da gobe. Toh Idan akace yau bukata na kudi ya tashi ba kudi, gobe wani bukatan ya sake tashi ba kudi, toh wani fa idan bukatunsa ya sake tashi jibi, toh duk abinda ya samu idan har zai samu kudi, toh shiga zaiyi. Ba yadda zaayi mutum yayi rayuwa ba tare da kudi ba, idan kuma ba aiki yi, toh dole a samu matsakar rashin kudi, idan kuma rashin kudi yayi yawa a guri toh fa dole zaa samu rashin zaman lafiya a wannan yanki.

Rashin aikin yi a arewacin Najeriya ya samo asalin daga rashin kishi na manyan arewa wadanda akasari ba talakawansu bane a gabansu. Su burinsu kullum talaka ya zauna cikin talauci da rashin ilmi saboda su ci gaba da mulki idan zasu sauka su kawo yaransu su ci gaba da mulki. Shi kuma talakawa suna amfani dasu gurin biyan bukatunsu gurin bangan siyasa da sauransu. Shiyasa duk hanyan da zasu bi suga talaka baya yalwala zasu bi. Domin tunaninsu Idan aka bar talaka cikin talauci duk abinda suka ce yayi domin ya samu wani abu, zaiyi.

Saboda haka ne basu son su kirkiro hanyar da matasa zasu samu aiki kokuma su samu Ilmi cikin sauki. Kama daga wadanda suka samu suka yi karatun zuwaga wadanda basu yi karatun ba, duk suna zaune ba aiki. Haka kullum sai kara kudin makaranta sukeyi domin dan talaka kada ya samu daman yin karatu balle yasa a ransa shima zai iya niman wani matsayi a gaba, sun manta da Allah ke ba da mulki.

Duk lokacin da masu mulki a arewacin Najeriya suka sa a raisu cewa zasu magance matsalar tsaro a arewacin Najeriya, zasu magance shi. Domin suna da daman da zasu fitar da tsare-tsaren da zasu magance matsalar rashin aiki da ta addabi matasa a arewacin Nageriya, sannan su fitar da tsare-tsaren da zasu magance matsalar rashin ilmi. Idan har aka magance wadannan matsalolin, toh da ikon Allah zaa samu saukin tashe-tashen hankali a arewa.

Ina Mafita

Idan har ana son a kauda matsalar tsaro a arewacin Nageriya dole sai masu mulki musamman gwamnonin arewa da yan kasuwan arewa sun fito da tsare-tsaren irin su gyara masana’antun (Companies) arewa da aka rufe da gina sabbin masana’antun (Companies) ta nan ne zasu rage matsalar rashin aiki da talauci a arewacin Najeriya.

Sannan a farnin ilmi, ya kamata gwamnonin arewa su fitar da tsarin samun ilmi kyauta daga primary zuwa secondary, sannan su inganta makarntun gwamnati, su kuma tilastawa iyayen yara da susa yaransu a makaranta, duk wanda baisa yaronsa a makaranta ba, toh gwamnati ta hukunta shi. Kuma su fitar da tsarin ba fulani makiyaya ilmin addini da na boko.

Sannan su rage kudin jami’o’i (Universities) da koleji da poli (Colleges and Polytechnic) ta yadda dan talaka zai iya biya. Sannan gwamnonin su dinga daukan nauyin karantun wayansu daga cikin yaran takawa.

Idan har akayi hakan, toh da ikon Allah zaa samu saukin matsalar ilmi da rashin aiki a arewacin Najeriya. Idan kuma aka samu saukin rashin ilmi da rashin aiki, toh Insha Allahu zaa samu saukin tashe-tashen hankula a Nageriya musamman a arewa. Domin duk wanda ya samu ilmi yana sa rai gobe da ikon Allah zai zama wani abu, haka wanda yake da aiki shima bazai so tashin hankali ba, domin zai hana shi zuwa aiki.

Amma idan masu mulki a arewa basu canja tunaninsu na su bar talaka a cikin talauci da rashin ilmi ba, toh su kiyaye fushin talakawa, lokacin da talakawa zasu juyo ta kansu, toh wallahi mutum yana ganin mulki, amma zai gudu ya bari. Domin duk lokacin da akace mutum ya tsinci kansa a cikin rashin ilmi da talauci, kuma yana ganin ga wanda yake zaluntarsa, toh komai na iya faruwa.

Wannan shine kadan daga cikin abinda zanyi tsokaci akai. Amma abubuwan da suke da alaka da matsalar tsaro a arewa suna da yawa.

Allah yaba shuwabanninmu ikon yi mana shugabanci nagari. Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu.

Allah ya bamu damina Mai albarka.

Share.

game da Author