Babban hafsan rundunar sojin Najeriya Tukur Buratai ya bayyana cewa daga yanzu tare da sojoji za rika yin aikin yi wa yara rigakafi a ajihar Barno.
Buratai ya fadi haka ne a taron horas da sojoji kan yi wa yara kanana allurar rigakafi wanda hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Barno (PHCDA) da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) suka shirya.
Ya ce rundunar ta dauki wannan mataki ne domin hanzarta kawar da cutar shan inna daga kasar nan ganin cewa hare-haren Boko Haram ya hana ma’aikatan kiwon lafiya zuwa wasu bangarorin arewa maso gabashin kasarnan.
Buratai yace domin samun nasara akan haka ya kafa wata batalia na sojoji mai suna ‘Theatre Command Buratai Initiative Task Force (TCBITF)’ domin kula da aiyukkan sojojin da aka horas don yin aikin rigakafin.
Yace suna sa ran cewa sojojin za su kammala wannan aiki a cikin watanni uku a maimakon watanni shida da aka tsayar.
Idan ba a manta ba a 2016 Buratai ya kafa kungiya irin haka mai suna BITF domin taya ma’aikatan kiwon lafiya yi wa yara allurar rigakafi a bangarorin jihar Barno da hare-haren Boko Haram ta yi kamari.
Bayanai sun nuna cewa BITF ta yi nasara wajen hana yaduwar cutar a jihar.
Buratai yace wannan karo rundunar sojin Najeriya za ta hada gwiwa da hukumar PHCDA, WHO, shugabanin kananan hukumomi da sarakunan gargajiyyar na wadanna yankuna domin samun nasara a aikin.
Bayan haka shugaban hukumar PHCDA, Sule Mele ya ce aiyukkan BITF ya sa jihar Barno ta yi tsawon watanni 32 babu labarin bullowar cutar.
Discussion about this post