Abin da ya sa ba mu ajiye kudade a bankuna -Inji wasu ‘Yan Najeriya

0

IBRAHIM GOMBE: “Ni dai ba na ajiya a banki. Ban taba yi ba, kuma ba zan taba ajiye ko sisi a banki ba har abada. Aljihu na da cikin mota ta sun ishe na rika ajiye ko ma nawa ne.” Haka wani mazaunin Abuja, mai suna Ibrahim Gombe ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Ibrahim dan hada-hada ne da ke kasuwanci daban-daban. Amma ya fi maida hankali a kan dillacin filaye. Ya kara da cewa.

“Ni dai ban ga dalilin da zai sa ba bata lokaci ina ajiya a gida ba. Wato ina da sauran harzuka, kuma ba na jimirin bata lokaci, domin yanzu sai ka ga ba harzuka hankali na ya tashi.

“Idan katin ATM di na ya makale ko na iske dogon layi a ATM ban iya hakuri, tuburewa zan yi kawai. Kai ni dai ban ga amfani bude asusun ajiyar kudi a banki ba.

Ba Gombe ne kadai ba ya ajiye kudi a banki ba. Wani bincike da aka gudanar a cikin 2018, ya nuna cewa ‘yan Najeriya milyan 39.6 da suka mallaki hankalin su, daga cikin miliyan 99.6, duk ba su ajiye kudi a banki.

Kididdigar ta kuma gano cewa kashi 44 ne maza, 56 kuma mata wadanda ba su kai ajiyar kudi a bankunan.

MATSALOLOLIN BUDE ASUSUN BANKI

Babbar matsalar bude asusun ajiyar banki ga masu karamin karfi, wato ‘Deposit Account’, ita ce jekala-jekalar ka’idojin da yawanci ke ba mutane haushi.

Za ka kai hoton ka a banki, sannan kuma idan har kudin ajiyar ka za su iya haura naira 200,000, to za bukaci ka kai katin shaidar kidaya, fasfo na fita waje ko lasisin tuki. Sannan kuma a ce sai ka kai rasidin kudin biyan wutar lantarki ko na ruwan da ka ke sha.

Da yawa wasu ba au da wannan, wasu akwai karancin ilmi ko rashin fahimtar ka’idojin. Sannan kuma dan za ka cire kudi kadan, sai ka bi layi a ATM.

Shi kuwa ATM sau da yawa akan samu dogon layi ko matsala ta sa a rike maka kati a lokacin da ka ke bukatar kudi da gaggawa.

Mutane da dama da PREMIUM TIMES ta tattauna da su, sun fi nuna damuwa da irin ka’idojin da banki ke gindayawa kafin mutum ya yi ajiya. Dukkan su kuma duk mutane ne masu karamin karfi.

Hassan lemon zaki ya ke sayarwa a Kasuwar Wuse, cikin Abuja. Cewa ya yi babu ruwan sa da wahalar zuwa banki kai kudi ko ciro kudi. Ya ce idan zai aika da kudi kauyen su, direba ya ke kaiwa a tasha, ko kuma wanda zai je garin, ko wanda ya zo daga garin na su zai koma gida.

Isiaka Kazim cewa ya yi jekala-jekala da bata lokaci ne ba ya so. Kai da kudin ka sai ka bi layi, kuma sai an gindaya maka ka’idoji.

Bincike ya nuna a yankin Arewa maso Yamma mutane kashi 62 bisa 100 ne ba su ajiya a banki.

A yankin Arewa maso Gabas kuma sun kai ka shi 85 bisa 100. Kudu maso Yamma su 19 bisa 100 ne kacal, yayin da Kudu masu Kudu na da 23 bisa 100, Kudu maso Gabas kuma 29 bisa 100.

Yankin Arewa ta Tsakiya na da kashi 31 bisa 100 na wadanda ba su ajiyar kudi a banki.

Share.

game da Author