Mazauna Katsina sun yi zanga-zanga bayan mahara sun kashe mutane 18

0

Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina, ya nuna alhini da ta’aziyya ga daukacin al’ummar Karamar Hukumar Batsari, inda mahara suka kashe mutane 18 a jiya Laraba da rana.

Masari ya yi jawabi ga wasu mazauna yankin da suka je har Gidan Gwamnati domin nuna damuwar su kan yadda aka bari ana ta kashe mazauna yankin a kullum.

Masari ya ce gwamnati na iyakar kokarin ta, kuma za ta kara rubanya kokarin da take yi domin ganin an kawo karshen wannan kashe-kashe.

“Na fi ku damuwa da wannan abu da ke faruwa, saboda na san sai Allah ya tambaye ni a Ranar Tashin Kiyama.

“Aikin mu ne mu kare rayuka da dukiyoyin al’ummar wannan jiha, amma kuma ga abin da ke ta faruwa. Mu na yi bakin kokarin mu.

“Ku ma dai shaida ne a kai na a duk lokacin da irin wannan hare-hare ya faru, ina kai ziyara, kuma ina shaida wa jama’a irin kokarin da mu ke yi domin magance wannan matsala.

“Gobe za mu je a gaban Shugaban Kasa mu baje masa wannan mummunar matsala da ke addabar mu a faifai.” Inji Masari.

Sai dai kuma Masari ya ce zanga-zanga ba ita ce za ta magance wannan masifa ba.

Ya roki jama’a su kwantar da hankulan su, domin gwamnati na yin kokarin ta wajen ganin an kawo karshen kashe-kashen.

Tun da farko, wanda ya jagoranci masu zanga-zangar mai suna Aminu Ruma, ya shaida wa gwamna cewa an kashe mutanen su 18 a gonakin su a garin ’Yargamji cikin Karamar Hukumar Batsari.

Ya kara yi wa gwamna bayanin cewa wasu manoman kuma sun bace, ba a san halin da suke ciki ba. shin sun tsre ne ko kuma an yi garkuwa da su.

Sannan kuma Aminu ya ce maharan sun sace shanun wadannan manoma.

Ya ce daga baya jami’an tsaro sun je sun kwaso gawarwakin suka kaisu Kofar Gidan Hakimin Batsari.

“Al’ummar Kananan Hukumomin Safana, Batsari da Danmusa ba za su iya yin noma a wannan daminar ba, saboda tsoron ’yan bindiga.’

Inji Aminu, sai ya yi kira ga gwamnati ta tashi tsaye domin ta ceci rayukan jama’ar da nauyin su ya rataya a kan gwamnatin.

Share.

game da Author