Manyan Ayyuka 10 da kwamitin Zartaswa ta amince ayi wa Babban Birnin Tarayya, Abuja

0

1. Gyara hanyoyin gefen titi na masu tafia a kasa a gundumar Wuse. Za a kashe naira biliyan 1.9 a wannan aiki.

2. Samar da tsarin wutan lantarki a shiya ta hudu. Za a kashe Naira miliyan 189.

3. Aiyukkan inganta walwalar jama’a a cibiyar gudanar da bincike ta shiya ta uku. Za a kashe Naira miliyan 197.

4. Zana fasalin gine-ginen inganta rayuwa ta shiyar G da H. Naira miliyan 118.5

5. Tsara hanyoyin magudanar ruwan bahaya a kan Naira miliyan 125. Naira miliyan 107

6. Gina sashen koyar da kimiya a babbar kwalejin ilimi dake Zuba.

7. Tsara fasalin aiyukkan ci gaban al’umma a gundumar Dawaki.Naira miliyan 259

8. Gina hanya mai tsawon Kilomita 41 da zai hada garuruwan Nyanya-Guruku-Mpape. Naira miliyan 174

9. Samar da na’uran gwaji ‘CT Scan Machine’ a asibitin gundumar Maitama a kan Naira miliyan 190

10. Sannan da tsara ababen more rayuwa ta gundumar Kubusa a kan Naira miliyan 179.

Share.

game da Author