AREWA: Sai Yawan Jama’a Ba Yawan Jami’a; Boko Ko Bokoko?

0

Cikin makon da ya gabata, jaridar Daily Trust ta buga yawan jami’o’i wadanda ba na gwamnati ba a fadin kasar nan. Sun yi dalla-dalla suka fayyace yawan jami’o’in da kowace Shiyyar Najeriya ta mallaka. Amma fa wadanda ba na gwamnati ba.

A nazari da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi bisa wannan rahota na yadda Arewa ta zama koma-baya wajen kafa jami’o’i, domin samun ingantaccen ilmin matasan yankin. Shiyyoyin Kudu maso Kudu, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas sun yi wa Arewa gaba dayan ta fintinkau wajen samar da wadataccen ilmin jami’a ga yaran da suke haihuwa.

Ilmin zamani, wanda a kasar Hausa farkon shigowar sa aka rika kira da sunan muzantawa, wata ilmin boko, ya shigo yankin Kudu masu Yamma a lokaci daya da shigowar addinin Kiristanci a Lagos, wajajen 1846.

SHIGOWAR ILMIN ZAMANI AREWA

An samu tazarar shekaru ba goma ba, ba talatin ko araba’in ba a tsakani, kafin ilmin zamani ya shigo Arewa. Lokacin da ya shigo din ma, ba a karbe shi hannu bibbiyu ba, sai aka kyamace shi kamar yadda ake kyamatar giya ko najasa.

Har sai da ta kai an rika kyamata da tsangwamar yaran da aka sa makarantun zamani a lokacin, wato ’yan makarkatar boko, maimakon ma a rika kiran su da ’yan makarantar boko.

Sannu a hankali kaka-gidan da Turawa suka yi a Arewa, bayan kifar da Daular Usumaniyya, sai karatun zamani ya fara karbuwa a Arewa, ko kuma a ce kasar Hausa, amma akasari a gidajen sarakunan gargajiya, hakimai da dagatai da sauran wadanda ke rabe da su.

Sai dai kuma an rika tilasta talakawa saka ‘ya’yan su makaranta ko da ba su so.

GUDUN KARATUN BOKO: ‘IYAR NISAN DAN KA, IYAR LADAR KA’

Wannan tilastawa da aka rika yi, ta haifar da gudun hijirar da iyaye suka yi da yaran su. Wato an rika dauke yara ana tafiya da su makarantun allo a garuruwa masu nisan gaske, da nufin tserewa daga kararun ‘Nasaranci’. Wato karatun boko.

A wancan lokacin an rika kyamatar karatun zamani matuka, har aka rika yi wa iyayen yara ‘fatawar-molon-ka’ cewa iyar nisan inda ka gudu da yaron ka, to iyar yawan ladar ka a wajen Allah.

Dalili kenan sai a dauki yaro daga Funtuwa ko Kankara a kai shi karatun allo Maiduguri ko Fataskum ko Gashuwa. Wasu kuma a lula Sakkwato da su ko Kano Kaura Namoda ko Zariya.

An rika yin gugumarar yin zugar kai yara karatun allo zuwa Maiduguri, har ta kai aka rika kiran Barno da sunan “Gabas”, kamar yadda ake kiran Makka da suna “Gabas.” Shi ya a lokacin idan wani ya tafi Makka, sai a ce ya tafi “Gabas, gaba da Gabas. Wato ya tafi gaba da Barno kenan.

Yawancin yaran da ake kai wa, ba su dawowa gida sai sun sauke Akur’ani. Wani a ranar da aka yi masa sauka za a yi masa aure, wani kuma sai shekara ta kewayo.

Da haka gidajen sarakai da na jikin su su ka rika yin zurfi a cikin karatun zamani, har suka rika fita Ingila, a daya gefen kuwa yaran jama’ar karkara na kara nausawa “Gabas” su na zuwa karatun allo.

A haka aka rika tafiya tsawon lokaci, Kudu na yi wa Arewa rata wajen karatu, su kuma gidajen sarautun gargajiya da makusantan su na yi wa sauran talakawan su tazara a karatun zamani.

ILMIN ZAMANI: AN DADE DA BARIN HAUSAWA BAYA –Ibramim Kurawa

A cikin wata hira ta musammnan da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi da Dakta Ibrahim Kurawa, wani masanin tarihi a Kano, a cikin Agusta, 2017, ya bayyana yadda tun farko aka bar Arewa, a baya a fagen ilmin zamani. Ga abin da ya ke cewa:

“Batun ilmi da ka fara yi, idan ka kalli lamarin, za ka ga cewa shi dama Bahaushe tun cikin karni na 19 har zuwa lokacin da Turawan mulki su ka shigo, bai damu da neman ilmi ba. Kai dai bar shi ga noma da fatauci kawai. Yayin da su kuma Fulani su ne malamai, su kuma ke karatun sauran fannonin ilmin musulunci.

“Wannan sai ya bai wa Fulani damar karkata zuwa ga ilmin zamani lokacin da Turawa suka shigo. Dama kuma shi kan sa ilmin zamanin a kasar Hausa dai ai ta hannun sarakunan gargajiya ya shigo, wadanda Fulanin ne, su ke mulki.

“Turawan Mulki sun rika tilasta wa sarakuna da sauran masu mulkin gargajiya su sa ‘ya’yan su makarantar boko. Dalibin farko a makarantar Gidan Danhausa a Kano, Bafulatani ne, sauran ma duk Fulanin ne duk ‘ya’yan masu mulki. Kai ko a firamare ma duk ‘ya’yan sarakuna da masu mulki ne su ka fara shiga, ko aka fara dauka.

“To haka abin ya rika tafiya. Ka ga ashe duk wanda ya kammala karatu, shi ma a gaba zai sa na sa yaran. Wadanda ba su fara karatu ba a lokacin, to za a dauki lokaci mai tsawo kafin su cimma tazarar da aka yi musu.

“Bahaushen farko da ya fara karatu a Makarantar Middle ta Kano shi ne Musa Iliyasu, ina zato a cikin 1939 ko 1940 aka sa shi makarantar. Malam Aminu Kano ma ya riga shi shiga kenan, domin shi tun a wajajen 1936 ya shiga Makarantar Katsina. To sai ka duba da kyau, Bello Kano, Dokaji, Ahmadu Matidan, Sani Dan Ciroma duk sun riga Musa Iliyasu shiga da shekaru kusan 20. Domin su tun a 1921 or 1922 su ka shiga. Dukkan su kuma Fualani ne idan ka debe Matidan, wanda shi Balaraben Kano ne.

“Dalibin farko a Kwalejin Barewa ina jin a cikin 1923, mai suna Abubakar, Bafulatani ne daga Sokoto. Shi aka fara dauka a tarihin Kwalejin Barewa. Shi ne ma ya zama Madakin Sokoto daga baya. Dalibi na hudun dauka, Ahmadu Matidan ma dan Kano ne, amma Balarabe. Ahmadu Bello shi ne wanda ya fara zuwa Kwalejin Katsina daga cikin jinin Shehu Danfodiyo. Ina jin wajajen 1926. Da wannan ilmin ne Fulani su ka fara shiga gaban Hausawa wajen aikin gwamnati da kuma mulki na siyasa a tarihin Nijeriya.”

Inji Kurawa, wanda ya yi Daraktan Bincike da Tattara Bayanai a zamanin Gwamnatin Ibrahim Shekarau, a Jihar Kano.

Bayan kafa jami’o’i a Arewa, ilmin zamani ya samu tagomashin karbuwa ganin yadda aka karbi mulki a hannun Turawa, kuma dukkan al’amurran tafiyar da mulki, gudanarwarwa da gwamnati duk sun koma karkashin ’yan kasa.

Amma duk da haka, kudu ta yi wa Arewa fintinkau ko a lokacin, domin ta kasance yawanci ’yan kudu ne suka yi kaka-gida a kan mukamai da yawa a Arewa.

AREWA: GA JAMA’A AMMA BABU JAMI’A

A yau ba jiya ba kuma ba gobe ba, idan aka auna yawan jami’o’in da ba na gwamnati ba, wadanda aka kafa a kudancin kasar nan, za a ga cewa an yi wa Arewa fintinkau a fannin neman ilmin zamani.

Ba don an yi sa’a gwamnonin jam’iyyar PDP sun gina jami’o’i na Gwamnatin Jiha a jihohin su ba, to da tabarbarewar ilmin jami’a a Arewa ya yi muni sosai yanzu a Arewa.

Gwamnonin PDP sun kafa jami’ar Jiha a Katsina, Gombe, Jigawa, Kano, Kaduna da sauran Jihohi da dama a Arewa. Wannan ya kara yawan jami’o’i a Arewa, amma kuma babu yawan masu zaman kan su kamar kudancin kasar nan

KUDU NA JAMI’A AREWA NA JAMA’A

Kididdiga ta tabbatar da cewa a yanzu haka akwai jami’o’I masu zaman kan su wadanda ban a gwamnati ba a Yankin Kudu maso Yamma har guda 36. Jihohin Kudu maso Yamma su ne Lagos, Ogun, Ondo, Oshun, Ekiti.

A jihohin Kudu maso Kudu kuwa akwai jami’o’i wadanda ba na gwamnati ba har 14. Jihohin Kudu maso Kudu sun hada da Bayelsa, Rivers, Cross River, Akwa Ibom.

Yankin Kudu maso Gabas da ya kunshi Enugu, Anambra, Abia, Imo da Ebonyi, akwai jami’o’i da ba na gwamnati ba har 13.

Amma kakaf a fadin Yankin Arewa maso Yamma, wato jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi da Jigawa, jami’a guda 3 ce rak ta masu zaman kan su.

Wannan yanki na Arewa maso Yamma shi ne ya fi yawan jama’a a Najeriya, yawan jama’a a Arewa, kuma shi ne ya fi samar da yawan kuri’u a zabe.

Arewa maso Gabas da ya hada da Gombe, Adamawa, Bauchi, Yobe da Barno, akwai jami’a 2 kacal.

Wannan yanki ne Boko Haram ya yi katuru, wanda ya samo tushen fitinar sa daga haramta karatun boko.

Yankin Arewa ta Tsakiya, da ya hada da FCT Abuja, Neja, Plateau, Benuwai, Nasarawa, Kwara, Kogi da Taraba, akwai jami’o’i masu zaman kan su guda 11.

Idan aka hada jimmila za a ga cewa a Arewa gaba daya akwai jami’o’i 16, su kuma Kudu akwai 63, duk masu zaman kan su, wadanda bana gwamnatin jiha ko na tarayya ba.

RASHIN JAMI’O’I A AREWA: Wani Babban Cikas

Baya ga tazarar da aka yi wa Arewa a jami’o’j masu zaman kan su, to wata babbar tazara kuma ita ce a addinance ma an yi wa musulmai tazara wajen kafa jami’o’i.

Wadannan jami’o’i na Kiristoci, ba fa addinin kiristancin zunzurutu suka koyarwa ba, sun a koyar da fannoninn ilmin zamani ne ne, kamar yadda sauran jami’o’in Gwamnatin Tarayya, na Jihohi da sauran na masu zaman kan su ke koyarwa.

Bincike ya nuna cewa akwai jami’o’i 32 mallakar manya-manyan coci-coci na kasar nan. Amma jami’o’i 2 ne rak mallakar kungiyoyin musulunci a nan kasar.

Sannan kuma baya ga jami’o’i 32 da coci-coci na Kiristoci suka mallaka, akwai ma wasu guda 15 a yanzu haka da wasu manyan coci-coci na kasar nan ke jira a ba su lasisi su kafa.

Karin tazara da aka yi wa Arewa wajen jami’a kuma ita ce jami’ar nan ta Gwamnatin Tarayya, wadda ake yin karatu daga gida, wato National Open University of Nigeria (NOUN).

Cikin watan Maris, 2019 ta yaye dalibai 20,799, amma kusan kashi 80 bisa 100 duk ‘yan kudu ne.

Sannan kuma ta na da dalibai sama da 400,000, amma kusan kashi 80 duk ‘yan kudu ne daliban. ’Yan Arewa ba su cika maida hankali wajen shiga jami’ar ba, sai cikin shekarun nan uku, bayan an bai wa Farfesa Abdalla Uba Adamu na Jami’ar Bayero ta Kano shugabancin jami’ar sannan aka karkato da hankulan ‘yan Arewa shiga jami’ar ta NOUN.

A karshe, cikin makon da ya gabata an bayyana cewa akwai jami’o’I 303 da ake son a yi wa rajista a kasar nan?

Shin nawa ne a cikin su za a kafa a Arewa? Kada fa mu Arewa ta shankake har sai Chana ta zo ta yi mana kaka-gida a fannin ilmi a Arewa, kamar yadda yadda suka yi kaka-gida a harkokin kasuwanci a Kano.

Share.

game da Author