Abin da ya sa Najeriya ba za ta janye tallafin man fetur ba a yanzu – Gwamnati

0

Gwamnatin Tarayya ta karyata ji-ta-ji-ta da ake watsawa cewa za a janye tallafin man fetur.

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta bayyana haka jiya Lahadi a lokacin da ta ke wa tawagar Najeriya bayanin sakamakon da ya biyo bayan ganawar ta da masu zuba jari da kuma shugabannin Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) da kuma Bankin Duniya.

An gudanar da taron ne a Birnin Washington DC na Amurka.

Zainab ta yi wannan furuci ne a matsayin martani da Bankin IMF da ya shawarci Najeriya cewa idan kasar na so ta tsira da mutuncin ta, to sai ta cire tallafin man fetur.

Wannan furuci ne ya sa masu motoci da sauran ababen hawa suka shiga rudun bin layin sayenn fetur don gudun kada a kara farashi a lokaci daya.

Su ma masu gidajen mai sun rika kulle wasu gidajen mai a tunanin su za a yi kari, domin su saida na su da tsada.

Haka a na sa bangaren, kamfanin NNPC ya rika yin shelar cewa akwai wadataccen mai a kasa, a daina ruguguwar cinkoson sayen mai.

Sai dai kuma wannan duk ta shiga ta kunnen jama’ar kasar nan ta ta fice, sai ma kara rincabewa abin ya yi a fadin kasar nan.

“Babu wani shiri na nan kusa ko na can gaba da gwamnatin tarayya ke yi wai da nufin janye tallafin man fetur.” Inji Minista Zainab.

“Jami’an IMF sun ce min zai fi wa Najeriya alfanu idan ta janye tallafin man fetur, sai ta yi wa jama’a aiki da kudaden.

“ A zahirin gaskiya kuma a ka’idance wannan shawara ce mai kyau. To amma a Najeriya ba mu da wani shiri da mu key i don a janye tallafin man fetur. Saboda ba mu ba tsara matakan da suka wajaba a janye tallafin ba, idan ma har janyewar za a yi, ta yadda za a fito da hanyoyin saukakawa ga jama’a idan an janye din.

“A yanzu dai babu wani shiri na janye tallafin man fetur. Idan ma har za a cire tallafin, to tilas sai mun rika zama da bangarorin da ke da ruwa da tsaki domin samo madadin hanyar saukaka wa jama’a idan har sai an cire tallafin.” Inji Zainab.

Share.

game da Author