ZARGIN DANNE BILIYOYI: Yadda EFCC ta damke jami’an Hukumar Tara Haraji 9

0

A yanzu haka akwai manyan Jami’an Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS), su tara da ke tsare a hannun Hukumar EFCC, da aka damke bisa zargin su da harkallar bilyoyin kudade.

Daga cikin manyaj jami’an da ke hannun EFCC a Abuja, har da Daraktan Harkokin Kudade na FIRS, Mohammed Auta.

Baya ga Auta, akwai wani darakta mai suna Peter Hena da ake zargin shi ma da hannun sa a badakalar.

Hena shi ne Daraktan Tsare-tsare Ayyukan FIRS, amma shi a halin yanzu an ce ba ya kasar.

Wata majiya daga EFCC ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana jiran duk ranar da Hena ya diro Najeriya, to za a yi masa kamun-kazar-Kuku.

Wani babban jami’in FIRS ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ai Hena ya fita kasar waje ne domin duba lafiyar sa, amma ba arcewa ya yi ba.

An hakkake cewa Hena ya na daya daga cikin ’yan gaban-goshin Shugaban Hukumar FIRS, Babatunde Fowler.

Har yanzu dai jami’an EFCC ba su kai ga gano shin ko Fowler din dungurugun ya na da hannu a harkallar ko babu ba.

Haka ita ma PREMIUM TIMES ba ta da wata hujja mai nuna cewa da sanin Fowler aka yi harkallar ta bilyoyin nairori.

Har zuwa yanzu dabu wani bayani dalla-dalla na badakalar bilyoyin kudaden da aka yi. Sai dai kuma ana binciken Auta da Hena da zargin karkatar da zunzurutun naira bilyan 6 na kudaden harajin da ya kamata a ce sun shiga aljihun gwamnatin tarayya.

Haka dai jami’an EFCC su ka bayyana.

Sannan kuma wakilin mu ya samu labarin cewa sauran jami’an da abin ya shafa su na aiki ne a bangaren kudi da kididdiga na hukumar ta FIRS.

PREMIUM TIMES ta binciko cewa jami’an su tara su na tsare ne a ofishin EFCC tun ranar 1 Ga Afrilu.

Sannan kuma PREMIUM TIMES ta sake gano cewa EFCC na ci gaba da wani sabon binciken a hukumar FIRS din dai domin bankado wasu badakala da harkallar bilyoyin kudaden haraji da aka karkatar.

Kakakin EFCC Tony Orilade, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa dukkan wadanda aka damke din suna can a tsare ofishin EFCC da ke Wuse 2, Abuja. Ya roki a dan ba shi lokaci domin ya yi karin bayani idan ya natsu.

Hukumar FIRS ce hukumar da ke tara kudaden haraji da sauran kudaden shiga na cikin gida ga gwamnatin tarayya.

Tun bayan nada Babatunde Fowler da Shugaba Buhari ya yi, FIRS ta ce an samu gagarimin ci gaban da ba a taba samu a baya ba.

Cikin 2018 FIRS ta ce ta tara kudaden shiga har naira tiriliyan 5.32.

Share.

game da Author