HARKALLAR FIRS: EFCC ta damke wasu darektocin hukumar FIRS dake da hannu a harkallar biliyoyin nairori

0

Hukumar EFCC ta damke wasu ma’aikatan hukumar tara haraji ta kasa, FIRS da ake zargi da hannu dumu-dumu a harkallar biliyoyin nairori kudaden harajin da ‘yan kasa ke biya.’

Cikin wadanda aka waske da akwai Babban Darektan harkokin kudi na hukumar, Mohammed Auta.

Baya ga Auta akwai wani babban darektan a hukumar mai suna Peter Hena da shima ya fada cikin wannan tarko. sai dai kuma shi hena baya ma kasar nan a yanzu sannan har yanzu ba a samu tabbacin ko akwai hannun shugaban hukumar Tunde Fowler ba ko kuma babu.

Kakakin hukumar Orilade Tony ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa lallai EFCC ta yi awon gaba da wadannan mutane amma da zararn ya samu karin bayani zai tuntubi sanarwa duniya.

Share.

game da Author