Atiku ya yi zargin kulle-kullen dage zabe a jihohin Borno, Adamawa da Kaduna

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari na kitsa wani shiri domin yin amfani da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta da nufin dage zabe a jihohin Barno, Adamawa da Kaduna.

A cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na dan takarar mai suna Phrank Shaibu ya fitar a jiya Talata, Atiku ya ce an kulla tuggun dage zaben a jihohin uku ne yayin wani taro na sirri da Buhari ya yi da gwamnonin jihohin uku a jiya Talata a Abuja.

Ya yi gargadin cewac duk wani yunkuri domin a haifar da tsaikon zabe a wasu jihohi, ba za a amince da shi ba.

Ya kara da cewa idan har aka dage zaben a jihohin uku, hakan zai ba gwamnatin APC damar yin magudi idan ranar da za a sake yin zaben a jihohin ta zo.

Ya kara da cewa PDP ta ci gaba da samun bayanan da ke nuna irin yadda APC ta makance ido rufe sai ta yi nasar a zabe ko ma ta halin kaka.

Sai dai kuma kakakin yada labarai na INEC ya ce bai san da zance ba, domin INEC ba ta halarci taron ba.

A cikin wata sanarwa da kakakin yada labaran sa, Ike Abonyi ya fitar da jijjifin asubahin yau Asabar, Secondus ya ce kara wa’adin ranakun zaben wani gagarimin tuggu ne da Shugaba Muhammadu Buhari ya kulla da nufin kankamewa a kan kujerar mulki, duk kuwa da cewa ‘yan Najeriya sun gaji da shi, sun a so ya su sauke shi.

Shugaban INEC ne ya yi sanarwar kara wa’adin sati daya kafin a gudanar da zabe.

“Biyo bayan bin diddigi na yin nazarin tsare-tsaren da INEC ta yi da kuma irin yanayin yadda shirin na ta ke tafiya har zuwa yanzu, da kuma dalilan alkawarin da INEC din ta dauka cewa za ta gudanar da sahihin zabe kuma karbabbe, wannan hukuma ta cimma matsaya cewa gudanar da zabe a ranar Asabar ba zai yiwu ba.

“Dalilin haka INEC ta dage zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dattawa zuwa ranar 23 Ga Fabrairu, shi kuma na Gwamna da na Majalisar Jiha da na Kananan Hukumomin FCT zuwa ranar 9 Ga Maris, 2019.”

Secondus ya kara da cewa PDP ba za ta taba amincewa da sakamakon zaben da ba a yi shi cikin gaskiya, adalci, kwanciyar hankali, zaman lafiya ba.

Ya ce ba za ta taba amincewa da magudi, tuggu, cin zarafin ‘yan adawa, yi musu barazana a wurin jefa kuri’a ko waskiya ba.

“Saboda sun ga cewa sun kasa cimma burin su na tuggun da suka kitsa don ci gaba da zama kan mulki, sai APC da INEC suka kulla kutunguilar dage zabe. Wannan kuwa babbar barazana ce ga dimokradiyyar kasar nan. Ba za mu amince ba.” Inji Secondus.

Secondus ya kara yin zargin cewa APC da INEC sun rika hada kai wajen kokarin yi wa zabe makarkashiya, ciki har da kona ofisoshin zabe a wasu jihohi inda kayann zabe suka kone kurmus, don kawai su kirkiro matsalolin da babu su.

Ya kuma buga misali da kisan mutane 66 da aka yi a jajibirin zabe a Kaduna, cewa shiri ne da APC ta yi domin kawai ta firgita jama’a har su ji tsoron fita su jefa kuri’a.

Share.

game da Author