Fadar Shugaban Kasa ta jaddada gargadin bindige barawon akwatin zabe

0

Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta jaddada gargadin da Shugaba Buhari ya yi cewa ya bai wa sojoji da ‘yan sanda umarnin cewa duk wanda ya sungumi akwatin zabe ya nemi ya gudu, to a bindige shi.

Buhari ya fadi haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce duk wanda ya saci akwati a zabe mai zuwa na ranar Asabar, to ita ce satar akwatin sa ta karshe.

Kakakin Yada Labarai na Buhari, Garba Shehu, ya bayyana cewa kamata ya yi jama’a su dauki wannan furuci a matsayin kakkausan gargadi.

Shehu ya ce idan aka yi duba da illar da satar akwati ke haifarwa, barayin akwati har kisa su ke yi kafin su saci akwati su tsere.

Har ya buga misali da yadda barayin akwati suka kashe mutane 26 a rincimin satar akwati yayin wani zabe da aka taba gudanarwa can shekarun baya a daya daga cikin jihohin Tsakiyar Najeriya.

Bai dai ambaci sunan jihar ba.

Ya ce kamata ya yi a jinjina wa shugaban kasa ba wai a rika yi wa furucin na sa fassara ta masu adawa ba.

Da ya koma kan PDP, Shehu ya ce shi bai san abin da ya sa duk suka damu ba don Buhari ya ce a harbe barawon akwati.

Ya ce duk mai gaskiya ba zai tsargu da wannan furuci na Buhari ba, sai ma ya jinjina masa.

Ya ce barayin akwati sun dade su na haddasa rikicin zabe a kasar nan, wanda kan haifar da asarar rayuka da dama.

Sai dai kuma masu adawa da wannan furuci na Buhari, sun ce furucin wani tafarki nev na mulkin kama-karya, domin dokar kasa dai hukuncin daurin watanni 24 ta gindaya wa barawon akwati.

Share.

game da Author