Dalilin da yasa Hukumar SSS ta soke gayyatar da ta yi wa jami’an INEC

0

A jiya Talata ne Hukumar Tsaro ta SSS, ta soke gayyatar da ta yi wa wasu manyan jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC uwa hedikwatar SSS ta Abuja.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa an gayyaci babban jami’i Okechukwu Ibeanu tare da wasu jami’ai hudu domin su je su bayar da ba’asi dangane da dalilin da ya kawo dage zabe.

PREMIUM TIMES ta kuma samu tabbacin cewa Ibeanu ya samu kiran waya ne daga SSS tun a ranar Litinin, inda aka umarce shi da ya kai kan sa hedikwatar SSS da ke Aso Drive, Abuja, a ranar Talata da karfe 2 na rana daidai.

Majiya ta kuma tabbatar da cewa su ma sauran jami’an hudu da SSS suka gayyata, duk ta wayoyin su ne aka kira su daya bayan daya ana sanar da su gayyatar da kuma lokacin da za su je din, karfe daya na ranar jiya Talata.

Sai dai kuma bayan da PREMIUM TIMES da wasu jaridu sun buga labarin gayyatar a jiya Talata, sai SSS suka soke kiran da suka yi wa jami’an na INEC.

Kamar yadda aka kira su daya bayan daya aka shaida musu gayyatar, haka aka sake kiran su da guda-guda ana sanar da su cewa an soke gayyatar da aka yi musu, ba sai sun kai kan su ba.

Amma kuma Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya shaida wa manema labarai cewa SSS ba su gayyaci ko da jami’in zabe guda daya ba.

Ya bayyana haka ne, duk kuwa da cewa SSS sun shaida wa wadanda aka gayyata din cewa sun sanar da Shugaban INEC gayyatar da suka yi wa jami’an na sa biyar.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin din ce dai Buhari ya ce zai sa a binciki dalilin da ya sa aka dage zaben.

Share.

game da Author