Atiku ya nemi a binciki harkalla a hukumar da surikin Buhari ke shugabanci

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira da a binciki rahoton harkallar da aka fallasa a Hukumar Inganta Kan Iyakokin Kasar nan, wadda surikin Shugaba Muhammadu Buhari ke shugabanci.

Atiku ya ce wajibi ne EFCC da ICPC da sauran hukumomin da abin ya wajaba a kan su su tashi tsaye wajen gudanar da bincike da kuma gaggauta gurfanar da wadanda ke da hannu a cikin harkallar.

Atiku ya yi wannan bayani ne a cikin wata takarda da ya aiko wa PREMIUM TIMES, ta bakin kakakin yada labaran sa mai suna Phrank Shaibu.

Ya ce idan ba a yi wa tubkar hanci ba, to batun yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari ke yi, zai zama tatsuniya kenan, matukar wasu masu kusanci da shi za su rika karya dokokin bayar da kwangiloli barkatai.

Premium Times ce ta fara fallasa wannan labari na yadda aka yi harkallar bai wa daruruwan kamfanonin da ba su cancanta ba kwangiloli a Hukumar Kula da Inganta Al’ummar Kan Iyakar Najeriya, wadda surikin Buhari, Junaid Abdullahi ke shugabanta.

Share.

game da Author