Ba a nuna son kai a yaki da rashawa – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na nema a sake zaben sa karo na biyu ne domin ya karasa dabbaka yaki da cin nhanci da rashawa da ya ke yi a yanzu.

Ya ce akwai kuma batun ci gaba da inganta tsaro da kara tabbatar da karfara tattalin arzikin kasa da ya ke yi.

Ya yi wannan jawabi ne a wurin taron ganawa da shi da Gidauniyar MacArthur da NTA da DARIA media suka shirya jiya Laraba a Abuja.

Buhari ya ce jam’iyyar APC ta sake tsayar da shi ne saboda ya cika alkawurran da jam’iyyar ta dauka a wancan yakin neman zabe da ya gabata.

Buhari ya ce babu wani ko da a wace jam’iyya ya ke da aka gabatar da kwararan hujja a kan a ce ba za a bincike shi ba.

Ya yi kira ga ‘yan jarida su rika fadada binciken su a kan yadda gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ke kashe kudaden su.

Share.

game da Author