Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a jiya Laraba cewa ba zai iya amsa tambaya a kan harkallar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje.
Buhari ya yi wannan waskiyar ce a wani taron ganawa da shi a jiya da dare, inda ya ce a yanzu maganar ta na a hannun kotu da majalisa, don haka magana a kan batun zai zama yi wa shari’a shisshigi kenan.
Sannan kuma Buhari ya shi bai sani ba asarkala da siddabaru aka yi wa bidiyon Ganduje ko a’a.
Kadia Ahmed ce ta tsara ganawar a Gidan Talbijin na NTA.
Buhari ya ce shi ma ya kalli bidiyon, amma kuma ya ce don Ganduje zai karbi kudin har sai ya rika cika fuskar sa da murmushi?
Daga nan sai Buhari ya ce ya ji dadin yadda ta kaya da aka fara binciken Ganduje a majalisa da kuma mika batun kotu, domin hakan ya sauke masa nauyin ya rika fitowa ya na yin magana a kan batun a bainar jama’a.
Ya ce ya na fatan zai idan ya je Kano lokacin kamfen zai gano bakin zaren da kuma sanin matsaya ta karshen batun.
An tambaye shi ko zai amince ya daga hannun Ganduje, ya yi tallar sa, sai ya ce ya na fatan kafin ya je Kano za a samu hukunci na karshe a kan zargin harkallar.