Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a gidan sa da ke Unguwar Asokoro, Abuja.
Ko da yake ba a asmi cikakken bayani kan dalilin wannan ziyara ba, Kakakin Atiku, Paul Ibe ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da wannan zumunci da kwankwaso yayi wa Atiku.
A cewar sa kwankwaso ya ziyarci Atiku ne kawai don yayi masa gaisuwan Sallah amma ba wai do wani abun ba.
Yace idan za a tuna Atiku baya gari a likacin bukin Karamar sallah, a dalilin haka ne ya sa sai yanzu ya sami damar isar masa da gaisuwar Sallah.
Kwankwaso ya isa gidan Atiku ne da karfe 8:30 na daren Asabar.
Discussion about this post