GANGAMIN APC: ‘Yan sabuwar PDP basu halarci taron ba

0

A bincike da muka yi a yau mun gano karara cewa kusan duka mambobin sabuwar PDP da ta narke ta shiga APC a 2015, basu halarci taron gangami na APC ba.

Da farko dai Rabiu Musa Kwankwaso bai halarci wannan taro ba, Murtala Nyako, da shugaban kungiyar Abubakar Baraje.

Sannan kuma da yawa daga cikin mambobin majalisar wakilai basu halarci taron gangamin ba.

Taron dai kamar yadda masu yin sharhi suka yi sun koka cewa ba a taba yin gangamin zaben wakilan jam’iyya ba musamman mai mulki da irin wanda akayi a yau.

A wasu runfunar har kona takardun zabe an yi, wasu kuma barkewa aka yi da rikici inda a kayi kaca-kaca da kujerun zama da rumfunar zabe.

Share.

game da Author