GANGAMIN APC: Wasu maniyyata sun gamu da ajalin su a Zaria

0

Wasu maniyyatan tafiya taron Gangamin APC da a yanzu haka ya ke kankama a Abuja, sun gamu da ajalin su, sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya ritsa da su a Zaria.

Maniyyata taron dai dukkan su daga jihar Kano suka fito. Kuma hadarin ya afku ne da safiyar Asabar a Zaria, tun ba su yi nisa da Kano sosai ba.

Cikin wadanda suka rasu din har da kansila mai wakiltar Mazabar Diso, da ke cikin Karamar Hukumar Gwale, a cikin birnin Kano, Abdulwahab Inuwa, sai kuma abokan sa biyu, Abdullahi Idris da Abubakar Diso.

Wani wanda hadarin ya afku a kan idon sa, mai suna Mustapha Lawal, ya shaida cewa mamatan konewa suka yi, saboda an kasa kashe wutar da ta kama motar, bayan ta fadi.

Motar, wadda kirar Honda ce samfurin CRV, ta rika wuntsilawa bayan da ta fadi a daidai kauyen Amaryawa, daf da shiga Zaria.

Ya ce su na cikin kici-kicin kokarin fito da su ne sai wuta ta tashi daga cikin motar.

Limamin Kano Sani Zahradden ne ya yi wa gawarwakin su Sallah a Babban Masallacin Kano.

Share.

game da Author