Yadda Minista Adeosun, Saraki, Dogara da Akanta Janar suka yi wa Naira biliyan 10 rabon-tuwon-gayya

0

Wannan harkalla ba za ta yiwu a gina rami a rufe ta, ba tare da mun bankado ta ba. Mu na da hakkin da ya wajaba a kan mu, wato sanar da ‘yan Najeriya cewa wakilan su da ke Majalisar Tarayya, a karkashin shugabancin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, sun karbi zunzurutun kudade har naira biliyan 10 daga asusun gwamnatin tarayya ta haramtacciyar hanya.

Wadannan kudaden fa na musamman ne, wai malami da kudin kida, domin ba su ma cikin naira biliyan 125 da aka ware musu a cikin kasafin kudi na 2017 domin hidindimun su na yau da kullum.

Ku ma ba su cikin wasu naira biliyan 100 da aka ba su domin yin wasu ayyukan a-gani-a-yaba a mazabun su, wadanda ayyukan ma ba yi suke yi ba, in banda raba wa ‘yan bangar siyasa garmar shanu da dabura da injin markaden tattasai. Saura kuma su watsa aljihun su.

Wadannan naira biliyan 10 da ake magana a yanzu, sun isa a biya ma’aikata dubu 45 masu karbar naira dubu 18, albashin su na shekara daya.

An tabbatar da cewa kudin ba su ma cikin kasafin kudi, kuma Shugaba Muhammadu Buhari bai ma san an zurara kudaden cikin aljifan su ba.

Ministan Kudi, Kemi Adeosun ce ta amince kuma ta bada izinin ba su kudaden, kamar yadda ta umarci Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris, shi kuma ya cika aiki.

PREMIUM TIMES da UDEME sun ci karo da wannan barankyankyama yayin da suke bin diddigin yadda ake kashe kudaden manyan ayyukan gwamnatin tarayya.

An kamfaci kudaden an raba wa ‘yan majalisa a matsayin wani kaso daga cikin naira bilyan 50 da wai za a ba su domin su yi aikin a-gani-a-yaba a mazabun su.

Wadannan fa ba su cikin naira bilyan 70 daga cikin naira bilyan 100 da aka ba su cikin 2017, domin ayyukan a-gani-a-yaba a mazabun su.

Baya ga wadannan naira bilyan 10 da aka ba su, an kuma dumbuza wa Saraki naira milyan 485 shi kadai, domin ya gina kananan makarantun sakandare a shiyyar mazabar sa ta Kwara ta Tsakiya.

A cikin kasafin kudin 2017, an ce a bai wa Saraki naira milyan 450 domin ya gina makarantun, amma da ka tashi fitar da kudin, sai aka kara dora naira milyan 35, wato ribar-kafa, wai kura ta taka kwado a wurin farauta.

Saraki da Dogara sun kirkiro hanyar karbar kudin daga wurin Minista Adeosun a saukake ne ta hanyar ba ta sunayen wasu ‘yan kwangila har 82, wadanda Saraki da Dogara suka ce wai su na bin majalisa bashi, kuma suka rattaba adadin da kowanen su ke bin majalisa bashi.

Wannan ne kawai dalilin da suka yi amfani da shi a mtsayin hujjar da Kemi ta sa hannu aka kamfatar musu kudaden.
Babu ruwan Adeosun, ba ta tsaya bata wa kan ta lokacin tambayar a kawo mata hujjojin ayyukan da ‘yan kwangilar suka yi ba, babu neman sauran hujjoji na zahiri da na badini ko ma daga Hukumar Tantancewa da Kula Da Kwangiloli ta Kasa, domin a ba ta satifiket na shaidar kammaluwar aiki.

Majiya da dama daga Ma’aikatar Harkokin Kudade sun tabbatar da cewa wannan harkalla ce kawai da kakuduba da kuma barankyankyamar da aka saba yi tsakanin ‘yan siyasa da ke kan mulki da kuma manyan ma’aikatan gwamnati.

Ita ma wata majiya daga Majalisar Tarayya ta tabbatar da cewa kudaden ba na wasu ayyuka ba ne, ‘yar-burum-burum ce kawai aka yi domin manyan wakilan majalisar su yi abin da Hausawa ke cewa gafiya-tsira-da-na-bakin-ki.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbatar da cewa kamfanoni 44 da Saraki da Dogara suka gabatar wa Kemi Adeosun daga cikin 82 din nan, ba su ma da rajista da Hukumar Kula da Kwangiloli ta Kasa, kuma babu su a cikin jerin Kididdigar ‘Yan Kwangila ta Kasa.

Karin bincike da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa wasu 17 ma daga cikin 44 din ko rajista da Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista ba su da ita.

Dukkan bangarorin Saraki da Dogara da PREMIUM TIMES ta tuntuba, sun kasa cewa komai.

Binciken da wakilinmu a Majalisa ya gudanar, ya tabbatar da cewa wasu ‘yan kwangilar a gaskiya sun yi ayyukan, amma fa tuni an rigaya an biya su tun tuni, amma kuma an jefa sunayen su a cikin wadanda aka ce wai su na bin bashi.

Share.

game da Author