Talakan Najeriya yana da bukata a kara wayar masa da kai akan darajar da tsarin mulkin siyasa ya bashi.
Gwamnatin siyasa tun daga ma’anar da masana siyasa suka bata kai tsaye tana nufin gwamnatin jama’a, ko kuma aiki da doka wasu kuma su kirata da tsarin gwaunati mai kare ‘yancin dan Adam.Ana kuma ce mata gwaunatin da masu rinjaye suke shugabantar marasa rinjaye.
Ma’ana, masu rinjaye sun hada har da ‘ya’yan jam’iya ba dole sai wadanda suke riqe da offisoshin gwamnati ba.
Su kuma marasa rinjaye sune wadanda suke gefe daya suka zira ido ake mulkar su.
Mulkin dimokaradiya yana mutunta lamba (Number) saboda shugaba baya bayyana sai ya samu babbar lamba a cikin zaben da akeyi duk bayan shekara hudu musamman a irin kasashen mu.
A zaben adalci, Kuri’a daya zata iya hanaka ko ta baka nasarar zama shugaban kasa ko gwamna ko sanata da sauransu shiyasa quri’a na firgita dan siyasa a filin zabe fiye da bindiga.
Talakawa ya kamata mu samu izza akan haka.
Babu dalilin da zai sa mu zubar da qimar da kundin tsarin mulki ya bamu akan kudin da bazasu iya canza mana rayuwa ba.Zaka iya karbar dubu dari ma ka za6i azzalumi daga baya kayi shekara hudu kana cikin fatara.Ai inaga ko mahaukaci yasan yin hakan babu riba balle kuma dattijo ko matashin da yake jira qasa ta gyaru don ya gina rayuwa mai kyau.
Saboda haka a za6e mai zuwa,kowa sai kun duba aikinsa kafin a sake zabensa idan kuma ya gaza za’a iya canzashi da wani ko dan APC ne don idan yana son jami’yar zai yi kokarin fito da kimar Buhari a idon duniya.